Sunday, 3 May 2020
LABARIN MUTUWA TA
INDAI KASAN KANAYIN SEX CHAT TSAYA KA KARANTA WANNAN SAQON.
ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI
TUNATARWA AKAN SALLAR JANAZA
•═══════❀💠❀═══════•
•═══════❀💠❀═══════•
2. KABBARA TA BIYU, Ana karanta Salatin Annabi ne ba wani salati na daban ba.
3. KABBARA TA UKU, Ana yin addu'a ne ga mamacin, mace ne ko namiji.
4. KABBARA TA HUDU, Za kayi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu.
DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama.
Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.
Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).
Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen.
Monday, 7 January 2019
WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA.
•═════════❀💠❀═══════════•
WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA.
•═════════❀💠❀═══════════•
FALALAR WANKAN GAWA
Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:
‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’
A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace:
”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin).
SHARUDDAN WANKAN GAWA:
Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:
{1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali:
Iyaye. kanne ko yayye “ya”yansa da sauransu).
{2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta).
{3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi.
YADDA AKE YIN WANKAN GAWA
Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali:
Sau Uku (3) ko
Biyar(5) ko
Bakwai(7) ko
Tara(9)).
Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (s.a.w) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A).
Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su zasuyi la’akari suga wanka nawa yadace suyi masa.
Da farko dai kafin a fara wankan da akwai abubuwa guda Uku (3) da za’a fara yi wa mamacin.
Sune kamar haka:
{1}. Za’a cire masa suturar da take jikinsa, amma za’a sami dan kyalle a rufe masa al’aurarsa.
{2}. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na bangaren mafuta biyu.
(Bawali da Gayadi).
{3}. Idan macece , za’a tsefe kitson da yake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba guda Uku).
Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.
Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba daya.
YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama saisu fara wankan.
Da farko dai zasu tanadi ruwa kashi Uku (3),
kowanne ruwa za'ayi wanka daya dashi.
(RUWAN FARKO)
Wannan wankan za'ayi wa mamacine wanka irin Wankan Janaba.
Da farko za’a fara yiwa mamaci alwalane, kamar irin alwalar Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da shakar hanci za’a shafa masa ruwane kawai a bakin da hancin.
Bayan anyi masa alwala, sai kuma azuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan. kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu.
(RUWA NA BIYU)
Bayan anyi masa wanka na sama wato na Janaba, sai kuma asami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin dashi.
Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, saidai za’a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun).
Bayan angama cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan.
(RUWA NA UKU)
Bayan anyi masa wanka na sama, wato na Soso da Sabulu, to sai kuma a sami ruwa na karshe wato na Uku a zuba Turare mai kamshi (Sosai) a ciki, sannan sai a wanke mamaci da shi.
Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to amma idan ba’a same shiba to za’a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai.
Bayan angama wankan Turaren, sai a tsane jikin mamacin asa masa Likkafani.
YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7), KO TARA (9).
Idan masu yi wa mamaci wanka sun zabi su yi masa wanka biyar (5), ko bakwai(7), ko tara(9).
To wanka na biyu(2) wato na soso da sabulu shi za su yi ta maimaitawa.
Amma dolene na Janaba shine a Farko, sannan na Turare shine a karshe.
MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU BIYAR (5).
{1}. Na farko shine na Janaba
{2}. Na biyu shine na soso da sabulu
{3}. Na uku shine na soso da sabulu
{4}. Na Hudu shine na Soso da Sabulu
{5}. Na Biyar shine na Turare.
YA UBANGIJI KASA MU CIKA DA IMANI KA KYAUTATA KARSHENMU.
Masu neman darussa irin wadannan zuku iya ziyartar wannan shafi kamar haka:
www.tafarkintsira.blogspot.co.ke
✔
Saturday, 5 January 2019
MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH.
Haqiqa wannan ciwo yajima yana haifar da matsaloli ga ma'aurata, wasu har takankai ga rabuwama gaba daya.
Wannan dalili yasa mukaga ya kamata shafin "TAFARKIN TSIRA" yayi rubutu akan wannan mas'ala.
ME YAKE KAWO BASUR ???
=========== ===========
Da yawan mutane suna kasa banbancewa meye basir da yawa mutum daga yaji cikinsa yana kugi ko yana ciwo sai yace basir yana damunsa, amma da yawa wasu cututtu suna kama da basir, kuma yana cutarwa da yawa.
Yakan sa sha'awar mutum ta bangaren jima'I ta dauke, ya kansa ciwon ulcer domin yana hana cin abinci, yana kuma kawo wata cuta wadda ake ce wa (sha'awatul-kaziba), shine mutum daya fara cin abinci sai yaji ya koshi.
Kowa da kowa zai iya samun wannan matsala ta Basir, maza da mata.
Amma ba acika ganinsa ga yara ba, anfi ganinsa ga manya, Kuma kowa zai iya samunsa a kalla sau daya a. rayuwarsa.
A manyan ma sai masu nauyi sosai, kamar mutane masu kiba.
A mata kuma za a ga basir ya fi yawa a lokacin da mace ta samu juna biyu, saboda nauyin da takara yayin daukar ciki, Idan ta haihu kuma ya baje.
A likitance basir shine ciwon jijiyoyi ko magudanan jini na dubura, na can ciki ko na waje-waje, wadanda suke kumbura su kuma yi ta ciwo.
Wasu abubuwan da ake gani suke kawo wannan ciwo sun hada da.
Yawan zama wuri daya na tsawon lokaci, yawan bayan gida mai tauri shi ma kansa jijiyoyi ko magudanan jinin dubura su kumbura su rika ciwo.
A dukkan wadannan yanayi, magudanan jinin suna kumbura, suja ruwa, wani lokaci su fashe.
Shiyasa mai basir wani lokaci yakanji zafi ko ciwo a dubura, wani lokacinma har da zubar jini.
GIDA NAWA BASIR YAKASU ???
Basir Ya kasu kashi uku.
Akwai na cikin dubura da kuma na kasa, akwai kuma mai tsuro wanda akan jishi yana saukowa, har sai an mayar da shi.
ILLOLI GUDA 20 DA BASIR KAN HAIFARWA DAN ADAM.
Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :
1.TSUWAR HANJI (INTESTINAL DISTURBANCE).
Zaka rinka jin hanjin cikinka na yawan tsuwa akowane lokaci.
2.KUMBURIN CIKI :Cikinka zai kumbure saboda toshewar hanji a sanadin dattin ciki da yawaitar girman kwayoyin cuta da rashin samun damar abinci ya yi saurin narkewa.
3.YAWAN TUSA (FREQUENT FLATUELENCE) : Zaka rinka yawan fitarda iska akai akai, wani iskan sai ka ce wanda ya ci mushe.
4.ZAFIN JIKI DA CIWON KAI : Jikinka zai rinka zafi ga kuma yawaitar ciwon kai wanda baya jin magani kamarsu analgesic.
5.RASHIN CIN ABINCI KA KOSHI : Basir na haddasa maka kaji baka iya cin komai,kusan komai kaci sai kaji ba dadi.Take ka koshi.
6.YAWAN ZUWA TOILET: Basir kansa kayi ta yawon zuwa toilet,idan kaje kuma kayi ta faman yunkuri da nishi sai zafin musiba da fitar majina ko jini dan tsirit.
7.RAMEWA : Basir kansa ka rame kamar mai ciwon qanjamau.
8.CIWON GABOBIN JIKI : Basir kan haddasa ciwon jiki da kowace ga6a ta jiki.
9.TASHIN ZUCIYA : Sai kaji kamar kayi amai,kana ta faman zubarda yawu.
10.FITAR BAYA : Duburarka zata fito waje (basir mai tsiro).
11.CIWO A CIKIN DUBURA : Sai kaji matsanancin ciwo ka kasa tsayawa ko zama.
12. DAUKEWAR SHAWA : Namiji yakasance kamar baima balaga ba, ita kuma mace batama san meye biyan bukata ba, duk tabi ta bushe ba ni'ima ba wata gamsarwa.
13. KAIKAYIN DUBURA : Basir kansa dubura ta tsage ga zafi da fesowar kuraje.
14.KURAJE GA MATSE MATSI : Basir kan haddasa irin haka amma mutane da dama suna tinanin kamar sanyi ne, to na sanyi ya sha banban dana basir, dan na sanyi akan ga zubar farin ruwa masu yauqi da wari kamar danyen kifi.
15. YANA MURDE HANJI : Ta yanda zai haifarda ru6ewar hanji da sauran cutukan ciki.
16. BAYAN GIDA MAI TAURI : Yana haddasa bayan gida mai tauri kamar duwatsu,kamar kashin dabbobi.
17.Basir na kawo ciwon baya.
18.Basir na haifarda (LIVER ABCESS)
19.Basir na haifarda Brain abcep,sai yakasance kamar kai hauka, kai yana ma haukata Dan-adam.
20.Yana hude hanji (intestinal ulceration, ga zafin ciki kamar mai ulcer).
HANYOYI KARIYA.
Hanyoyin sun hada da yawan motsa jiki da yawan hada ganyayyaki a cikin abinci da yawan cin ’ya’yan itatuwa, Wadanda duka sukan sa bayan gida laushi.
MAGANI DA YARDAR ALLAH.
Idan ciwon basir ya hanaka gamsar da iyalinka wato ya kashe maka jijiyoyin azzakari basuda karfi ka jarraba hada wannan maganin.
Kanemi sassaken dinya da saiwar tsada da saiwar sabara, amma yakamata sassaken dinyar yafi yawa sosai, sai a dakasu sai a gauraya waje guda.
Kullum arinka dibar cokali daya a dafa da ruwa kofi daya sannan a tache asha har zuwa mako daya (1week).
Idan kuma basir din yana tsirowa to sassaken dinyar za a samu a dafashi tun yana danyensa Sannan a surka ruwan daidai misalin yadda baza a chutu dashi ba.
Sannan a juye acikin bahon wanka, sai a rinka zama aciki wannan yana kone basir mai tsiro cikin gaggawa.
A bangaren maganin islamic kuma asamu Garin Habbatus Sauda kamar cokali 3 sai a hada da Garin sassaken Dinyar shi kuma cokali 1 a saka garin citta cokali daya sai a samu zuma kamar copy karami a zuba agauraya akarinqa shan cokali2 safe da rana da yamma wato sau uku a rana.
Idan tsirowa basir din yakeyi za a iya samun garin Hulba da bagaruwa da kuma garin sassaken dinya ka rinka dafawa ana zama acikin ruwan zafin
wadannan magungunan dukkansu sun inganta domin mun dade da jarrabasu.
Mai neman taimako irin wannan zuku iya ziyartar wannan shafi kamar haka:
www.tafarkintsira.blogspot.co.ke
ALLAH (S.W.T) yabada lafiya.
Monday, 2 July 2018
ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA
ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA
A lokacin da kake ‘ko’karin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai bu’katar ka nazarci wasu abubuwa wad’anda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.
*FARKON HA’DUWAR KU.
*YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
FARKON HA’DUWAR KU
A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?
Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.
Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kud’inka. A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.
A dukkan lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.
Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da wad’annan abubuwa kamar haka;
*Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.
*Matu’kar tana son ka za ta kasance mai kar’bar shawarar da duk ka bata kuma za ta kasance mai son abun da kake so.
*A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna ‘kosawa da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa lokacin da za ku yi sallama.
*Idan har ka saba kiran ta a waya matu’kar ta damu da kai idan ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka ta ji ko lafiya, idan ma bata kira ba saboda wani dalili bayan ka kira za ta yi kalamai na nuna ta yi kewar ka.
*Idan har tana son ka a kullum za ta ke ‘ko’karin yin abun da zai faranta ranka, za ta ke ‘ko’karin guje wa abun da zai sa ka yi fushi.
*A lokacin da soyayyarku ta yi nisa zata iya bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe ta.
*A lokacin da ka nuna ‘bacin ranka a kan wani abu da ta aikata da ba dai-dai ba, a yayin baka ha’kuri da shawo kan ka za ta iya zubar da hawaye.
*Zata ke ‘ko’karin bayyana ka ga ‘kawaye da kuma ‘yan gidansu.
*Zata ke ‘ko’karin turo maka da kalamai na soyayya.
*Zata kasance mai tambaya a dangane da ‘yan uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani da ta san kuna a tare.
*Za ta ke damuwa da damuwarka.
Irin wad’annan abubuwa da sauran ire-iren su duk zai kasance ta na nuna maka su.
YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
Akwai bu’katar ka fahimci yaya yanayinta da kuma halayyarta suke,
*Shin tana da jan aji ne da yawa? wanda hakan ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu abubuwa da zaka iya tinanin wula’kanci ta yi maka, amma da sannu matu’kar ka iya allonka za ka wanke.
*Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana son ka, idan ka yi ha’kuri da sannu soyayyarka za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da sannu tulu yake fashe wa.
*Koda a ce bata da son kud’i farkon soyayyar ku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta son abun hannunka zai rinjayi son da take yi maka na gaskiya, an dai kuma ce kyauta tana ‘kara soyayya, amma kuma komai ya yi yawa to zai kawo matsala.
Don Allah idan kun karanta , ku turawa wasu suma su karanta su amfanu daku.
Allah (S.W.T) yakawo mana dauki ya kuma sa mudace.
Daga shafin TAFARKIN TSIRA
Sunday, 22 April 2018
MENENE FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN ???
FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.
««fatawa ta 10 »»
MENENE FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN ???
AMSA
-----
Azumin Ramadan yanada falaloli da yawa.
Daga cikin falalar azumin sun hada da:-
1. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace:
Manzon Allah {S.A.W} yace:
"Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).
2. Yazo a hadisai da dama cewa:
Dukkan aikin Dan Adam nasane Malaikune suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake sakawa wanda yayi shi (hadisin ya tabbata acikin targhib wattarhib, juz'I na farko shafi na 75).
3. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan Abdullahi (R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.} cewar:
Azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa dashi daga wuta.
3. Sannan hadisi ya tabbata daga Mu'azu dan Jabal (R.A.) cewa:
Hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin bazan nuna maka kofofin alheriba ?
Sai yace na'am ya Rasulullah.
Sai yace azumi garkuwane.
4. Sannan akwai hadisin Abi Umamata (R.A.) yace:
"Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa"
(dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578).
6. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah.
7. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama sannan a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira.
(Kuduba Sahihul Bukhari 1899).
8. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace:
"Warin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren Al-miski a wurin Allah.
Hadisine sahihi.
9. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin Sa'ad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace:
Acikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin kiyama, babu wanda zai shigeta sai su.
Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake shiga
(Kuduba Sahihul Bukhari 1896).
Tirmizi yakara bayani a cikin riwayarsa cewar wanda ya shigeta bazaiji kishin ruwaba (Qishirwa ba) har abada.
YADDA AKE WARWARE SIHIRI.
YADDA AKE WARWARE SIHIRI.
TAMBAYA:
Assalamu alaikum.
Dan Allah malam a fitar dani daga cikin duhu gameda abin da yake damuna.
Mahaifiya tace taje gurin Boka ayi mata naganin ciwon mara da yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara guda da rabi, amma likitoci sunyi scanning sunce ba komai tosai Bokan yace mata asiri akayi mata, kuma zaiyi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma zata kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata bata aminta da Bokan bane.
Shiyasa Nakeso kabani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini ?
Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita ?
Wassalam nagode malam Allah yaqara basira.
(Daga Binta Umar).
AMSA
-----
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, tabbas ba'a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani.
Wasu malaman sunyi bayani cewa:
Ana iya warware sihiri ta hanyar karanta wadannan ayoyi kamar haka:
1- Ayatul-Kursiyyu.
2- Quliya.
3- Ikhlas.
4- Falaki da Nasi.
5- Sai kuma ayah ta: 117 zuwata 122, cikin Suratul A’araf.
6- Sai kuma Ayah ta: 79-81 cikin Suratu Yunus.
7- Sannan sai Ayah ta: 65-70 cikin Suratu Dhaha.
Za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka dashi a waje mai tsafta.
Haka ake magance sihiri cikin yardar Allah.
Bai halatta ki taimaka mataba, wajan bada wadannan kayan da boka yanema duk da cewa mahaifiyarkice.
Saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.
Ya wajabta gareki kayi mata nasiha cikin hikima, kisanar da ita cewa:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
“Duk wanda yaje wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah bazai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in”
Muslim ya rawaito acikin hadisi mai lamba ta: 2230.
Kinga idan mutum ya mutu acikin wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita.
Sannan awani hadisin kuma yana cewa:
“Duk wanda yaje wajan boka ya gaskata abin daya fada, to tabbas ya kafurce da abinda Annabi Muhammad yazo dashi”
Kuduba Sunanu-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta: 3904, kuma Albani ya inganta shi.
INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZAKI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.
Allah Shine mafi sani.
FIFIKON ANNABI (S.A.W) DA AL'UMMARSA AKAN SAURAN AL'UMMATAI.
FIFIKON ANNABI (S.A.W) DA AL'UMMARSA AKAN SAURAN AL'UMMATAI.
Lokacin da Allah ya kusantar da Annabi Musa (A.S) izuwa gareshi yayi zance dashi akan dutsen Sinaa' sai ya tambayi Allah cewa:
"Ya Ubangiji shin duk cikin bayinka kuwa, akwai wanda yafini girma awajenka ?
"Naga ka kusantar dani gareka, kuma gashi kanayin zance dani"
Sai Ubangiji yace masa:
"Na'am!
Annabi Muhammadu (S.A.W) yafika girma awajena".
Sai Annabi Musa (A.S) yasake cewa:
"To Ya Ubangiji, indai Annabi Muhammadu (S.A.W) yafini girma awajenka, to shin Al'ummarsa fa sunkai Banu Isra'eela girma awajenka?"
"Naga ka yanka musu teku sun ratsa ta cikinsa Ka tseratar dasu daga Fir'auna da Jama'arsa.
Sannan ka ciyar dasu daga Mannu da kuma Salwa."
Sai Ubangiji yace masa "Na'am.
Al'ummar Muhammadu (S.A.W) sunfi Banu Isra'ila girma awajena"
Sai Annabi Musa (A.S) yace:
"Ya Ubangiji inaso kanuna min Al'ummar Muhammadu (S.A.W) ingansu".
Sai Ubangiji yace masa:
"Ya Musa bazaka gansu ba, Saidai zan jiyar dakai sautinsu".
Sai yace:
"To ya Ilahee"
Sai Ubangiji yayi kira cewa:
"Yaku Al'ummar Muhammadu (S.A.W)! ku amsa kiran Ubangijinku!"
Sai suka amsa alhali sannan suna cikin tsatson iyayensu maza, da kuma mahaifun iyayensu mata har izuwa ranar Alkiyama.
Suka ce:
"MUN AMSA MAKA YA UBANGIJI!
TABBAS KAINE UBANGIJINMU DA GASKE.
KUMA MU BAYINKA NE DA GASKE".
Sai yace:
"KUNYI GASKIYA, TABBAS NINE UBANGIJINKU DA GASKE. KUMA KU BAYINA NE DA GASKE.
HAQIQA NAYI MUKU AFUWA (Na gafarta muku). KUMA NABAKU (FIFIKO) TUN KAFIN KU ROKENI.
"DUK WANDA YA SADU DANI DAGA CIKINKU YANA MAI SHAIDA CEWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, ZAI SHIGA ALJANNAH".
(Ibnu Mirdawaihi ne ya ruwaito daga Abdullahi bn Abbas (R.A).
Ya Allah kaqara tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W).
HIKAYAR MALAMI DA BARAWO
KUNJI BAYIN ALLAH NAGARI!!!
Wata rana wani malami yana sallar dare a gidansa, sai barawo yashiga zaiyi sata barawon ba musulmi bane, sai zuciyarsa taraya masa cewa yashiga dakin malamin.
Yana shiga yasami sabuwar riga ya dauka yagudu malamin yana idar da sallah sai yaga ansace masa riga, sai yafara addu'ah yana mai cewa:
Ya Allah kafini sanin wanda yasace min riga, Allah ka rufa masa asiri.
Yaci gaba dayin addu'ah ya Allah kasa wannan satar tazama alkhairi a gareshi.
¥ Bayan wata (4).
Malam yahada kudi yatafi kasuwa zai sayo riga sai yatarar ana rigama akan rigarsa da barawo yasace masa, ga barawo da riga sannan kuma ga mai saye sannan ga jama'ah sun taru ana rikici.
Malam yace lafiya kuwa ???
Mai saye yace kawai don nace yakawo shaida domin kada insayi rigar sata irin wannan mai kyau a walakantani a gari.
Barawo yagane malamin, shima kuma malam yagane rigarsa.
Sai malam yace ba barawo bane, ni shaidane.
Mai saye dai shikam sai yafasa sayan riga.
Sai malam yabiya kudin riga yadawo gida da kayarsa.
Barawo jikinsa sai yayi sanyi saboda malamin yarufa masa asiri.
Sai yabi malam har gida ya musulunta.
Kunga wannan shine sanadai Arzukin da malam yaroka masa a wajen Allah (s.w.t).
Ya Allah kasamu daga cikin bayinka masu afuwa da kuma yafiya.
KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.
KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.
1. Ka karanta:
"Laa ilaaha illallahu, wahdahu laa shareeka lah, lahul-mulku, wa lahul-hamdu, wa Huwa alaa kulli shai'in qadeer"
kafa 100 bayan sallar asuba.
2. Idan kazo kwanciya, Ka karanta Suratul Ikhlas (Sura ta 112), Falaq (Sura ta 113), Nas (Sura ta 114), ka tofa a hannu, sannan, ka shafe a jikinka gaba daya.
Ka yi haka sau 3.
3. Ka karanta:
Hasbiyallaahu laa ilaaha illaa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-Arshil Azeem"
Kafa 7, da safe da kuma yamma.
4. Ka Karanta:
"Bismillaahil lazee laa yadurru ma'asmihi shai'un fil-ardi walaa fis-samaa'i wa Huwas samee'ul Aleem."
Kafa 3 da safe da kuma yamma.
5. Ka rinka cin Dabino guda 7 (irin wanda ake cema ajwa na madina) kullum da safe.
6. Ka karanta:
"A'uzu bi kalimaatil-lahit taammaat min sharri maa khalaqa."
Kafa uku da safe da yamma.
7. Ka karanta Amanar rasulu zuwa karshe lokacin da zaka kwanta barci.
(Suratul Baqara ayata 285 zuwa ta 286).
8. Ka rinka kwanciya da alwala.
Allah kabamu kariya da kariyarka, sannan ka rabamu daga sharrin azzalumai.
Malam ban wuce shekaru goma sha daya ba a duniya, amma na shiga bandaki sai naga wani jini yafito min, har yafara jika karamin wandona (pant), to malam shin wannan jinin haila ne ko kuma na cutane ?
☀TAMBAYOYIN TAFARKIN TSIRA☀
««fatawa ta 63 »»
Assalamu Alaikum.
Malam ban wuce shekaru goma sha daya ba a duniya, amma na shiga bandaki sai naga wani jini yafito min, har yafara jika karamin wandona (pant), to malam shin wannan jinin haila ne ko kuma na cutane ?
Don naga kamar shekaruna basu kai nayi jinin haila ba.
Allah yayi makaalbarka a rayuwa.
(Daga Fatima Abbas).
AMSA:
-----
Ameen
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 ko 09-60 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50 wannan ya danganta da irin yanayinta da kuma wurin da take zaune.
Malamai sunyi sabani shin akwai wata shekara ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin daya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za’a kira shi jinin haila ba ???
AMSA
-----
Darimi -Allah yayi masa rahama- yace bayan ya ambaci sabanin da akayi:
(Wannan duk kuskure ne awajena).
Domin abin lura shine samuwar jinin, don haka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekarane ya wajaba a sanya shi yazama haila”.
Wannan abin da Darimi yafada shine daidai saboda Allah da manzonsa sun rataya hukunce- hukuncen jinin hailane da samuwarsa, basu kuma iyakance wasu shekaru na musamman ba, kamar yadda Ayah ta: 222 a Suratul Bakara take nuni.
Wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili na daga litttafin Allah ko daga sunnar Manzonsa, ba’a kuma samu ba.
Saboda haka jinin da kika gani sunansa jinin haila, kamar yadda malamai suka fada duk jinin daya fito daga gaban mace sunansa jinin haila mutukar ba’a samu wani dalili da yake nuna cewa na cuta neba.
Allah Shine mafi sani.
Don neman karin bayani kuduba:
(Dima’uddabi’iyya, shafi na: 6).
DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU.
DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU.
Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Wanda ya karanta Alqur'ani yana cikin Sallah, ga kowane harafi yanada lada dari.
Kuma wanda ya karanta Alqur'ani ba cikin Sallah ba amma yana da alwalla, shi kuma ga kowane harafi yanada lada Ashirin da biyar.
Kuma wanda ya karanta Alqur'ani batare da alwalla ba, ga kowane harafi yanada lada goma".
Wannan hadisin akwaishi acikin MUJALISUL ANWAR da DURRATUN NASIHINA.
Allahu Akbar!
Alqur'ani babban kundi!
Gulbi kake ba'a kai gacinka!
Kowa ya rike ka yadace!
Gaka Haske! Gaka Shiriya!
Gaka Hanya mikakkiya har aljannah!
Allah Sarkin rahama !
Alqur'ani yanada harafi guda DUBU DARI UKKU DA ASHIRIN DA UKKU, DA DARI SHIDDA DA SABA'IN DA DAYA. (323,671).
Don haka ga yadda lissafin yake:
WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI CIKIN SALLAH.
Yana da lada: 32,367,100. Miliyan Talatin da biyu, da dubu dari ukku da sittin da bakwai da dari daya.
WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BA CIKIN SALLAH BA AMMA YANADA ALWALLA.
Yana da lada: 8,091,775. Miliyan takwas da dubu casa'in da daya da dari bakwai da saba'in da biyar.
WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BATARE DA ALWALLA BA.
Yana da lada: 3,236,710. Miliyan ukku da dubu dari biyu da talatin da shidda da dari bakwai da goma.
Don haka ya kamata ace kowane musulmi yana samun kashi guda daga cikin su, a kalla ya sauke Al-qur'ani sau daya duk bayan wata biyu.
Duk wanda baya karanta alqur'ani, to yanzu dai yaga irin hasarar ladar da yakeyi.
Shi kuma wanda yake karanta alqur'ani, to yaga dai irin ladan da yake samu.
Allah yakara sanya rabonmu a ciki, yakuma kara bamu ikon cigaba da karantawa.
www.tafarkintsira.wapka.me
FALALAR YIN SALATI GA ANNABI (S.A.W).
FALALAR YIN SALATI GA ANNABI (S.A.W).
Abdur-rahman bn Auf (R.A) yace:
Naga Manzon Allah (S.A.W) yayi sujjada, kuma ya tsawaita sujjadar, sannan yadago kansa, sai na tambayeshi gameda haka ???
Sai yace;
"Jibrilu (A.S) ne ya sameni, sai yace dani.
Duk wanda yayi maka salati daya, Allah (S.W.T) zaiyi masa salati, (sau goma).
Wanda yayi maka sallama, Allah (S.W.T) zaiyi masa sallama, (sau goma).
Shine nayi sujjada ga Allah don godiya".
Wannan hadisin Ahmad bn Hanbal ya ruwaito shi acikin MUSNADU hadisi mai lamba 1664.
Sannan Baihaqi ya ruwaito shi hadisi mai lamba 157.
Kuma Hakim ma ya ruwaito shi a juzu'i na daya hadisi mai lamba 550.
Babban abin lura acikin wannan hadisin shine.
Shin me yasa Annabi (S.A.W) yayi sujjada ?
Me yasa yake godiya ?
Amsa itace, yayi sujjada kuma yayi godiya ne saboda wani babban alheri yasamu masoyansa watau mu al'ummarsa.
Wannan yanuna tsananin son da Annabi (S.A.W) yake yi mana, da tsananin bukatar da yake da ita, ta yaga mun sami rahama.
Don haka kada muyi watsi da wannan damar da muka samu.
Mu kara gode ma Allah (S.W.T) daya sanyo mu cikin al'ummar wannan babban masoyi namu, wanda yake murna idan alheri ya samemu.
Kuma mu kara son wannan babban masoyi namu, mahaukacin so, baji ba gani, mu bishi ido rufe kawai, duk abinda ya inganta daga gareshi kada mutsaya wasa, mu kama, mu damka, mu rike, muyi tayi kawai, wannan itace mafita.
Duk wanda bai fahimta ba yanemi karin bayani gun malaminsa.
Sannan daga karshe mukama salatin Annabi muyi tayi, a ko ina muke kuma ko cikin wane hali muke.
Allah ya kara mana son Ma'aikin Allah (s.a.w).
Mutum nawa zasu amsa mini ???
Akwai wani zamani zai zoma al'ummata
MANZON ALLAH KENAN SARKIN GASKIYA !
MANZON ALLAH (S.A.W) Yace:
Akwai wani zamani zai zoma al'ummata (acikinsu) duk wanda yariqe addininsa zai zama kamar wanda yariqe garwashin wuta.
MANZON ALLAH (S.A.W) yace:
Nan gaba kad'an al'ummomi zasu zagayeku (ku musulmai) kamar yadda jama'a ke zagaye kwanon abinci.
Sai sahabbai suka tambayi manzo cewd:
Shin bamuda yawane a lokacin ?
Sai yace kunada yawa amma yawanku taron tsintsiyane babu shara kuma nan gaba kad'an Allah (s.w.t) zai cire kwarjinin da kuke dashi acikin zukatan abokan ga'barku (kafirai) kuma yasanya muku rauni.
Sai yace son duniya da qin mutuwa.
MANZON ALLAH (S.A.W) yace:
Wasu shekaru masu yaudara zasuzo wayanda acikinsu zakaga ana qaryata mai gaskiya kuma ana gasgata mai karya.
Mai ha'inci zaiyi zamansa cikin kwanciyar hankali, amma za'a riga cutar mutumin kirki.
'Yan uwa yanzu a wane irin yanayi muke ciki ???
ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA.
Sunday, 14 January 2018
SOYAYYA ITACE:
MAGANIN IN INA.
MAGANIN IN INA.
Ga wani taimako da wani bawan Allah yanema acikin wani group namu sai nake ganin yadace nabada amsa anan saboda za'a sami mai buqata irin tasa ga abinda yake cewa kamar haka:
SALAM INA NEMAN TAIMAKO GA WANDA ALLAH YAHORE MASA, ALLAH YA JARABCENI DA KINKINA WATO (STARMER) SHIN TANADA MAGANI KUWA DOMIN NA JARRABA MAGUNGUNA DABAN DABAN ALLAH YASA MUDACE IDAN DA WANDA ZAI TAIMAKAMIN TO INA MARHABAN DA HAKAN.
ALLAH YASA A DACE:
TO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH.
Kadinga tofa wannan aya a ruwa Qafa 7 kanasha.
"RABISH RAHLY SADRY, WA YASIRLY AMRY, WAH-LUL UQDATAN MIN LISANY, YAFQAHU QAULY"
(Tana cikin suratud DAAHA ayata 24 zuwa ta 28.
Insha Allah za'a dace.
Nima wallahi Qanwata da muke uwa 1 uba 1 tayi kuma da wannan Allah ya taimakemu ta daina.
WALLAHU A'ALAM.
INA SAMARI DA 'YAN MATA ???
INA SAMARI DA 'YAN MATA ???
Ku karanta wannan.
Lallai hadisai sun tabbata wadanda a cikin su Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake kwadaitar da mai neman aure yaje ya ga wadda yake nema, domin wannan shi zai janyo hankalinsa zuwa son ta har ta kaishi ga auren ta.
Daga ciki akwai hadisin da Abu Huraira radhiyallahu anhu yace:
"Na kasance tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sai wani mutum ya zo, ya ba shi labarin cewa ya auri wata mace daga cikin matan Madina.
Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:
“Shin kaje ka ganta?
”sai yace:
‘A’a ban jeba.
’Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace dashi;
Kaje ka ganta, saboda akwai wani abu a cikin idanun mutanen Madina.
Haka kuma hadisi ya tabbata daga Jabir Ibn Abdullahi radhiyallahu
anhu yace:
"Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:
Duk wanda zai nemi auren mace daga cikinku.
idan ya samu ikon ya kalli abin da zai ja hankalinsa ga auren ta, toya aikata".
A bisa wadannan dalilai wasu malamai suke ganin cewa za a iya kallon duk wani sashe na jikinta wanda zai janyo hankalinsa ga auren ta, amma ban da al`aurarta.
Wannan shi ne abin da Imamul Auza’i ya fada.
Saidai mafi yawan malamai suna ganin cewa, abin da ya halatta a kalla kawai,
shine fuskarta da tafin hannunta, domin su ne suke nuna kyawun mace.
Kuma sun shardanta cewa;
Wannan kallon ya kasance don jan hankali
ne zuwa ga auren ta kawai, ba don janyo fitina da tayar da sha`awa ko faruwar fasikanci ba.
Haka kuma shari`ar Musulunci ta hana mai
neman aure kadaita da wadda yake nema a zaure ko daki ko falo ko kuma kadaita kowace irin nau’i ce.
Domin Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam yace:
"Kada wani mutum ya kadaita da wata mace, kuma kada wata mace tayi tafiya, face tare da ita akwai muharraminta…
Sauda yawa zaka ga samari suna raka yan matansu bakin titi, da sunan wayewa!
To mu sani cewa kadaita, tana jawo fitina da waswasin shaidan.
Don haka, masu yin zance suyi hattara da kadaita da matan da suke so.
Yana daga cikin mummunar al`adar da ake aikatawa a wannan zamani yadda ake
yawaita zance kullum da surutai marasa fa`ida.
Haka kuma yana daga cikin dabi`un da basu kamata ba, yi wa mace alkawarin karya da nufin wai za a cika mata bayan aure.
Haka kuma akwai masu yin aron sutura ko abin hawa, yayin zuwa
zance don yaudara, duk wannan bai kamata ba.
Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu yace:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce:
"Alamomin munafiki guda
uku ne!
1. Idan ya yi zance sai yayi karya.
2. Idan an bashi amana sai yayi ha`inci.
3. Idan yayi alkawari sai ya saba.
Saboda haka muna nasiha ga `yan’uwanmu mazaje dasu nisanci wadannan siffofin marasa kyau.
Haka kuma su ma `yan’uwanmu mata su ji tsoron Allah, domin babu abin da ke sa a yi musu karya da yaudara, sai kwadayi da son abin duniya.
Haka kuma yana daga cikin munanan al`adu a wannan zamani, yadda wasu ke kwaikwayon
al`adun Turawa na yin hannu da wadda suke so su aura, ko rike hannunta
da sauran abubuwan da
suke kai wa ga aikata alfasha da fasikanci.
Bayan kuwa hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (R.A) tace:
Na rantse da Allah!
Hannun Manzon Allah (s.a.w) bai taba shafar hannun wata mace ba yayin mubaya’a, sai dai yana
mubaya’a da su ne ta hanyar maganayace:
Na karbi mubaya’arku.
Don haka idan har
Manzon Allah (s.a.w) da Allah ya aiko shi zuwa ga dukkan talikai, kuma yayi masa kariya daga aikata sabo ya guji wannan, don mene ne kai za ka fada cikin wannan
mummunan aiki alhali baka da wani abin koyi fiyeda Manzon Allah (s.a.w) ba.
Haka kuma yana daga cikin munanan dabi`u a wannan zamani, ta yadda
wasu masu neman aure suke wassafawa
abokansu kyawu da kuma siffofin macen da suke so su aura.
Idan kuma ba sa son ta ko
kuma an samu sabani a tsakaninsu, sai su rika aibata ta ga mutane kuma su rika tona
asirinta, haka su ma matan suke aikatawa.
Kai! Abin ma har ya kai a tsakaninsu suna aikawa juna munanan sakwanni da hotuna na batsa ta hanyar wasika a waya (text message) da yanar
gizo-gizo (Internet), ta
yadda za ka ga `ya`yan musulmi suna aikawa da hotunansu tsirara a shafin Facebook da Twitter da 2go da sauransu, Wa
Iyazu Billah!
Wannan abu
ya kai matukar muni dalalacewar tarbiyya.
To, a nan ina so a
fahimci cewa; tushen mafi yawan matsalolin da
muka ambata, suna faruwa ne daga iyaye, saboda sakacinsu ga sha`anin tarbiyyar `ya`yansu wanda yake kai su ga nadama lokacin da
nadamar ba za ta yi amfani ba.
Nasiha ta ga `yan’uwa mata kuma ita ce: su ji tsoron Allah, su rike addininsu da mutuncin gidajensu, kada don suna jin wayewar kai, ko kiraye- kirayen Turawan yamma na `yancin mata ko zurfin ilimin zamani, ya sa mace ta zubar da
mutuncinta ko ta bayar da kanta ga wanda ba mijinta ba.
Domin wannan zai kai tane kawai zuwa ga halaka.
Da fatan zamuyi aiki da wannan nasih.
MU'UJIZA MAI GIRMA.
MU'UJIZA MAI GIRMA.
----------------------------
Wata rana akusa da Khaibar (wani garin yahudawa ne).
Manzon Allah (s.a.w) ya kwanta, ya 'dora Kayinsa abisa Qafafun Sayyiduna Aliyyu (r.a) alhalin ana saukar masa da WAHAYI adaidai lokacin.
Har akayi La'asar amma shi Sayyiduna Aliyyu bai yiba.
Har rana tafadi sannan Manzon Allah (s.a.w) ya farka.
(Wahayin ya idda sauka).
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya tambayeshi cewa:
"YA ALIYYU shin kayi sallar la'asar ne ?"
Sai yace "A'a banyi ba YA RASULALLAH.
(Alhali rana ta riga tafadi).
Nan take sai Manzon Allah (s.a.w) yacira hannuwansa masu Albarka, ya roki Allah yana cewa:
"YA UBANGIJI!!
ALIYYU YA SHAGALTU NE ACIKIN BIYAYYARKA DA BIYAYYAR MANZONKA.
DON HAKA (YA ALLAH) KA MAIDO MASA DA RANA (domin yayi sallah)."
Sayyidah Asma'u (wacce ta ruwaito hadisin) tace:
"Tun da farko mun ga lokacin da rana tafadi.
Amma Wallahi nan-da-dan sai muka ganta ta dawo da baya, ga haskenta nan a doron Qasa da duwatsu"
ALLAHU AKBAR!!!
Kunji fa!
Ranar ta dawo da baya har Manzon Allah (s.a.w) da Sayyiduna Aliyyu (r.a) sukayi sallarsu suka idar.
Sannan ta sake komawa ta fadi.
Duk wanda yayi kokwanta akan mu'ujizar Annabi, imaninsa mai rauni ne.
Ibnu Katheer ne yakawo wannan hadisin acikin ALBIDAYAH WAN-NIHAYAH juzu'I na 6 shafi na 80, 81, da kuma na 85.
Sannan aduba TAFSEER na Imamul Qurtubiy juzu'I na 5 shafi na 97.
Allah kaqara mana Soyayya Muhammad Rasulullah.
KARANTA WANNAN QISSA KUJI MAKIRCIN SHAIDAN.
KARANTA WANNAN QISSA KUJI MAKIRCIN SHAIDAN.
Wani mutumi ne yatashi tunda wuri yashirya tsaf! Ya canza tufafi yayi alwala domin zuwa masallaci yayi sallar asuba.
Yana kan hanyarsa tazuwa masallaci, kwatsam! Sai ya
fadi, tufafinsa suka lalace.
Sai yatashi ya kakka6e jikinsa ya koma gida ya canza kaya, ya sake alwala, ya kuma nufi hanyar masallaci.
Yana isowa inda yafadi dazu sai yasake faduwa!!
Tufafinsa suka sake lalacewa ya kakka6e ya koma gida ya canza wasu tufafin, yasake alwala, ya kuma kama hanya zuwa masallaci.
Koda ya iso inda ya fadi harsau 2 dinnan kawai sai yaga wani mutum rike da fitila, dasuka gaisa sai mutumin yace dashi:
"Dazu naga kafadi har sau 2, akan hakane nazo domin in haska maka".
Suka kama hanyar masallaci su 2, sai da suka isa, sai wanda yafadi dazu yashiga masallaci, yakuma kira wanda yake haska
masa yashigo suyi sallah tare; amma yaqi yashigo,
Yayi~yayi yashigo masallaci amma yaqi !!!
Daga qarshe sai mutumin yace masa:
"Da farko dai ni shedan ne.
(sai mutumin yaji tsoro dajin wannan magana).
Yaci gaba da cewa:
A lokacin daka fito zaka masallaci nine na kayar dakai akaro na farko.
Sanadiyar faduwar dakayi baka damuba kakoma kashirya kasake dawowa.
Sai Allah ya gafarta maka zunubanka gaba daya!
Akaro nabiyu nasake kayar dakai.
kakuma yin hakuri kasake dawowa baka yanke shawarar yin zamanka a gidaba.
Sai Allah kuma ya gafartawa iyalanka zunubansu!!
Shiyasa naji tsoron idan nasake kayar daka Allah zai gafartawa mutanen kauyenku zunubansu gaba daya.
Shiyasa nayi musu hassada da bakin ciki, domin kada agafarta masu nafito da fitila har
na tabbata ka isa masallaci lafiya batare daka fadiba, balantana
agafartamasu, ni kuma ina baqin ciki naji UBANGIJI yayiwa bawansa gafara)"..
Tofa kunji irin Qiyayyar da Shaytan yakeyi mana.
Yaa Allah kasamu a cikin masu Rinjaye akansa.
SHIN KO YA HARAMTA A SADU DA MACE MAI CIKI.
Malam naji wasu mutane na fadar cewa baya halatta idan matar mutum tana da ciki yayi jima’i da ita har saita haihu menene gaskiyar maganar ???
AMSA
-----
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan’uwa ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki.
Saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi cewa:
“Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa”
Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba: 1847
Ibnul kayim jawziyya babban likitan nan na musulunci yana cewa:
“Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa”
Kuduba Tahzibus-sunan 1\193 .
Saidai masana likitanci a wannan zamani suna cewa:
Ba’a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zaifi kyau ta dinga yin goho yayin da zasu sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron.
Sannan yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a Qaranta saduwa dasu a wadannan lokutan.
WALLAHU A'ALAM
AKWAI ABIN AL-AJABI GA RAYUWAR WANNAN DABBA MAI YAWAN GASKE.
AKWAI ABIN AL-AJABI GA RAYUWAR WANNAN
DABBA MAI YAWAN GASKE.
Bashi da zuciya ajikinsa amma yana iya rayuwa.
Kamaluddeen Kmc Wrote:
Lizard wanda hausawa sukafi sani da hausa kadangare yanada abin Al'ajabi tattare dashi.
Ganin yadda Allah yayima kusan kowace dabba zuciya ajikinta domin pumping din
blood dinsu.
Amma shi wannan dabba lizard wato kadangare shi bashida zuciya ajikinsa.
kuma ahaka yake rayuwa abinsa.
Ikon Allah ikon gaske.
Yadda Allah yayi masa hikima ganin bashida zuciya shine, kamar yadda zuciya take amfani wajen pumping din jini ajikin mutane da dabbobi.
To shi kuma zafin ranane yake iya pumping din blood dinsa.
Shiyasa idan rana tafito da safe zakaga kadangare
yana kwance ajikin
katanga garu rana tana bugunsa.
Yana amfani da zafin ranane wajen narka jininsa tayadda jinin zai iya zagawa tako ina
ajikinsa.
Wannan shiyasa zakaga kullum zaka lizard kadangare akan katanga garu yana bin zafin rana.
Ko kuma zakaganshi a sararin waje a fili yana bin zafin rana.
Kuma shiyasa zakaga baya fitowa waje a lokacin sanyi, kullum yana cikin rami ko kuma lungu saboda yafi musu
dumi da zafi a lokacin, saboda su samu jininsu karya daskare domin yana daskarewa sai mutuwa.
Shiyasa suke mutuwa idan sanyi yadame su.
Duba littafin animal life encyclopedia volume7. shafi
na 48, ko littafin adventures the
reptiles and amphibians shafi na 146.
Jama.a kuga hikimar Allah ajikin kadangare, bashida zuciya amma hasken rana shine yake aiki a matsayin zuciya a gareshi.
Ya Allah ka kara mana imani dajin tsoron ka.
Ya Allah kasa mudace da rahamarka.
MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI ???
MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI ???
AMSA
-----
Zakkar fidda kai sunnah ce daga cikin sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Manzon Allah da kansa ya aikata ta, hakama sahabbansa sun aikakata.
Za'a iya fidda ita kafin ganin wata, domin sahabbai sun aikata haka.
Ana fitar da zakkar fidda kai ga kowane musulmi, yaro da babba, mace da namiji, 'Da ko kuma bawa, kowane mutum mudun nabi hudu.
Amma abin mamaki mafi yawan mutane basu damu da fitar da itaba, saboda da'awar talauci.
HAKIMAR ZAKKAR FIDDA KAI
TSARKAKE MAI AZUMI:
Tana tsarkake mai azumi daga kuskuren daya aikata acikin azuminsa na ramadan kamar zantukan banza, zagi, kallon haram da sauransu.
SANYA WALWALA AZUKATAN 'YAN UWA MUSULMI:
Zakkar fidda kai tana sanya walwala a zukatan 'yan uwa musulmai ta yadda babu wani dan uwa da zai nemi abinci da zaici a ranar farin cikin sallah yarasa, da sauransu.
SUWA YA KAMATA SUYI ZAKKAR FIDDA KAI ???
Hakika zakkar fidda kai ta rataya akan dukkan musulmi mai 'yanci ko bawa, babba ko yaro, namiji ko mace.
TAMBAYA ???
SHIN YA TABBATA WANDA BAI FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAIBA, ZA'A RATAYE AZUMINSA, BA ZA'A KARBA BA HARSAI RANAR DA YA BAYAR ???
AMSA
A'a Wannan hadisin bai tabbata daga bakin manzon Allah ba.
Hadisi ne mai rauni, kuma duk mutumin daya bari aka sauka daga idi bai bayar ba, hukuncin zakkarsa kamar sauran sadaka ne ba zakkar fidda kai bace.
WALLAHU A'ALAM
YA ALLAH KADATAR DAMU
Dan Allah kuyi Like da share dinsa saboda yan uwanku su amfana.
Allah ya hadamu acikin ladan baki daya.
JIN QAMSHI A LOKACIN SADUWA.
JIN QAMSHI A LOKACIN SADUWA.
.
Haqiqa jin kamshi a lokacin saduwa yanada muhimmanci sosai dan yana daya daga cikin abubuwan da zaisa jin dadi da dandanon Jima'I kuma rashin jin kamshi zaisa megida yarika kyamar kusantarki koda kuwa yana sonki sosai.
Dan haka 'yan uwa mata akula please.
Duk macen da keson idan tana saduwa da mijinta KAMSHI yarika tashi tanemi wadannan abubuwa kamar haka:
1.Miski.
2.Ambar.
3.Ganyen magarya.
4.Rihatul hubbi.
5.Zam-zam.
Saita hadesu wuri guda akwano saita dan tafasasu, idan yahuce sai tanemi buta ta dan kara Ruwa saita rika shashshafa shi har gefenta, zuwa cinyoyi.
Inshaa Allah zaki sha mamaki.
*Wallahu A'alam*
JIN QAMSHI A LOKACIN SADUWA.
JIN QAMSHI A LOKACIN SADUWA.
.
Haqiqa jin kamshi a lokacin saduwa yanada muhimmanci sosai dan yana daya daga cikin abubuwan da zaisa jin dadi da dandanon Jima'I kuma rashin jin kamshi zaisa megida yarika kyamar kusantarki koda kuwa yana sonki sosai.
Dan haka 'yan uwa mata akula please.
Duk macen da keson idan tana saduwa da mijinta KAMSHI yarika tashi tanemi wadannan abubuwa kamar haka:
1.Miski.
2.Ambar.
3.Ganyen magarya.
4.Rihatul hubbi.
5.Zam-zam.
Saita hadesu wuri guda akwano saita dan tafasasu, idan yahuce sai tanemi buta ta dan kara Ruwa saita rika shashshafa shi har gefenta, zuwa cinyoyi.
Inshaa Allah zaki sha mamaki.
*Wallahu A'alam*
KUCI ANAN MUNCI ACAN:
KUCI ANAN MUNCI ACAN:
.
ANYA WANNAN MAGANAR GASKIYA CE KUWA ?
.
A yayin daka tsinci kanka cikin wadata to, kada kayi tinqaho da fankama gamida toroqoqo tare da yiwa sauran mutane kallon hadarin kaji.
Wannan duniya ba komai bace, shiyasa zakaga Allah yana bawa kowa ita, sabanin lahira.
Babu wanda yake samun ta face mumini.
Hatta a watan azumi, akwai wanda yake sahur da buda baki da kala-kalan abinci na gani da fada, sakamakon wadatar dukiya da Allah ya bashi, yayin da zakaga wani wallahi da sauran tuwo ko ragowar kunu yake sahur, kuma yayi buda baki da qwayoyin dabino da kunu da qosai, haka zai yi haquri har zuwa asubahi kuma ya dauki wani azumin a hakan.
To, koma dai acikin wacce tawaga Allah ya jefaka, haka zaka bautawa Allah yadda ya cancanta ka shiga aljanna, haka kuma zaka keta alfarmar shari'a ka sabawa Allah ka shiga wuta.
(Wal'iyadhu Billah).
Akwai wata magana da malam bahaushe yakeyi wai: KUCI ANAN MACI ACAN!
Hmm wannan magana akwai gyara, ba sunnar Allah bace cewa duk wanda yaci anan ba zaici acan ba.
Kuma wanda bai ci anan ba zaici acan, wannan ba haka bane.
Zai iya yiwuwa:* kaci anan kuma kaci acan.
Ko kaci anan kuma baza kaci acan ba.
Ko kuma bakaci anan ba kaci acan.
Ko kuma bakaci anan ba kuma baza kaci acan ba.
(Wal'iyadhu Billah).
Ba alama ce ta rashin rabo a lahira ba don kasamu arziqi a duniya, ba kuma alama ce ta rabo a lahira ba don baka samu arziqi a duniya ba, kuma kasani zaka iya rayuwa cikin talauci da quncin rayuwa a duniya kuma ka shiga wuta a lahira.
Haka kuma zaka iya rayuwa cikin wadata da yalwar dukiya a duniya kuma ka shiga aljanna a lahira.
ko sabanin haka.
Talauci da wadata duk jarabawa ce Allah yake yiwa bayinsa a rayuwa.
Kada karudu da wannan magana ta malam bahaushe ka yaudari kanka cewa wai tunda baka samu arziqi a duniya ba to, a lahira kune 'yan aljanna!
"Hmmm sannu dan gata"
Wallahi zaka yaudari kanka, kaidai kaci gaba da bin dokokin mahaliccinka sauda-qafa, yi-nayi, bari-na bari, sannan ka qasqantar da kai a gareshi, wannan shine mafita kuma ita ce hanyargaskiya.
Idan bakabi Allah (S.W.T) ba, azaba zai maka, babu ruwansa da talaucinka.
*************************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, yaqara mana imani da taqwa tareda qanqame shiriyar Manzon Allah.
(Sallallahu Alaihi Wasallam).
KAYI KOMAI BA KOMAI AL-JANNAH TA MAI RABO CE:
KAYI KOMAI BA KOMAI AL-JANNAH TA MAI RABO CE:
Mene ne ingancin wannan maganar?
A haqiqanin gaskiya muna wasa da Allah, ta inda muke furtawa da harsunanmu abubuwan da ke fusata Ubangiji, kuma muna sane muke yin haka.
Amma da yake Allah Ta'ala mai rahma ne sai yake qyalemu baya azabtar damu da zarar mun furta munanan kalmomi, sai yabamu lokaci har mu tuba.
Amma wannan bai kamata yazame mana hujjar cigaba da furuci barkatai ba, ya zamana duk abinda muka gadama kawai sai mu furta.
Babu yadda za'ayi wanda yasan daraja da qimar addini ya furta wannan kalma, saboda muninta.
Amma baya wuce dayan biyu:
1. Imma dai jahilci:
Saidai jahilci baya iya zama hujja ga bawa, dolene bawa yayi Ilmin sanin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Addininsa.
2. Ko kuma tashen balaga da rud'in shaid'an.
'Dan'uwa ka auna wad'annan kalmomi domin gano munin su:
Ka yi komai ba komai aljannah ta mai raboce.
Ma'ana:
Ka aikata duk abinda kakeso ko mene ne kuma komai muninsa a wurin Allah.
Misali:
Ka yi zina
kayi luwad'i.
ko kiyi madigo
kayi qarya.
kayi caca.
kaci riba.
kaci haram.
ka yi kisan kai.
kasha giya da sauransu.
ka aikata duk wani nau'in aiki da kakeso komai muninsa, kada kaji komai ai aljannah ta mai raboce.
(Wal'iyadhu Billah).
Wannan fa shine irin munin da wadannan kalmomi ke qunshe dasu.
Da yawan masu furta wadannan kalmomi sune 'yan uwanmu matasa 'yan bana-bakwai, wadanda gigin balaga ke dibarsu, da kuma 'yan mata wad'anda kejin kansu ta fuskar sha'awa kuma babu tarbiyya, sai wasu daga cikin zaurawa wadanda basu kwankwadi tarbiyya ba.
Shiyasa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana mana a cikin hadithi cewa:
(( Mafi yawan abubuwan da ke kai mutane wuta shine furucin harsunansu.
Don haka mu kiyayi Allah, mu daina furta kalmomi barkatai wad'anda bamu san ma'anonin su ba, saboda gudun furta kalmar dake fusata Ubangiji, saboda haka mu dinga sanin kalmomin da zamu dinga furtawa, domin kaucewa afkawa halaka.
***************************
Allah ya shiryar da mu akan hanya madaidaiciya, ya yafe mana kusa-kuranmu wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba, ya kuma tsare mu daga afkawa halaka.
Friday, 12 January 2018
JAN HANKALI GA MASU KOTAN KURCIYA A SALLAH DA MASU SHIGA MASALLACI A GUJE SABODA TSORON KARSU RASA RAKA'A.
JAN HANKALI GA MASU KOTAN KURCIYA A SALLAH DA MASU SHIGA MASALLACI A GUJE SABODA TSORON KARSU RASA RAKA'A.
.
.
.
.
.
.
WAJIBI NE MU TSAYA MUKOYI SALLAH IRIN YANDA MANZON ALLAH (SAW) YA KOYAR DOMIN ITACE ZATA KAIMU ALJANNAH.
MUTUMIN DA MANZON ALLAH (SAW) YASAMU YANA BALLAGAZAR SALLAH A MASALLACI YACE, JEKA KASAKE SALLAH BA HAKA AKE SALLAH BA, YAYI YA SAKE HAR SAU 3.
ANNABI (SAW) YACE, BAHAKA AKE SALLAH BA, YA TSAYA YA KOYA MAI SALLAH YACE:
DA KAMUTU A WANNAN HALI TODA KA MUTU BA AKAN IRIN SALLAR MUHAMMAD (SAW) BA.
"LAU MATA ALA HADHA MATA ALA GAIRI MILLATI MUHAMMADIN."
ANNABI (SAW) YANA CEWA:
صلو كما رأيتموني أصلي
SALLOO KAMA RA'AITUMOONI USALLI."
WATO KUYI SALLAR KAMAR YANDA KUKAGA NAYI.
(MA'ANA YANDA NA KOYAR).
WADANDA KE SHEKAWA DA GUDU ANA SALLAH GUDUN KARSU RASA SALLAH SUJE CIKIN SAHU SUNATA HAKI BA NATSUWA.
MANZON ALLAH (SAW) YACE, IDAN KUN TAFI ZUWA SALLAH KUJE CIKIN NATSUWA ABINDA KUKA RASA SAIKU CIKA.
Saboda haka dan Allah mu kiyaye.
MAGANGANUN ANNABI (S.A.W) GAMEDA LAFIYAR JIKI (2).
MAGANGANUN ANNABI (S.A.W) GAMEDA LAFIYAR JIKI (2).
1. Amfanin Nonon saniya.
Ku shaayar da Matayenku masu ciki Nonon saniya, domin yana qara qarfin Hankalin Jariri.
2. Amfanin danyen dabino.
Idan mace ta Haihu, yazama farkon abinda zataci shine Danyen dabino mai
zaqi da kuma busashe, domin da ace akwai wani abu dayafi wannan kyau ga mai jego, tabbas da Allah madaukaki ya shayar da Maryama (A.S) shi a lokacin da ta haifi Annabi Isa (A.S).
NI 'YAR GATACE A WAJEN BABATA.
NI 'YAR GATACE A WAJEN BABATA.
'YAR MAI KUDI DA 'YAR TALAKA 'YAN MAKARANTAR PRIMARY
••••••••••••••
Wata rana 'yar mai kudi ta tara kawayenta 'ya'yan
talakawa tana cewa dasu:
UWATA me arzikice
saboda tasayi mota ana kawomu
makaranta kuma muna fita yawo akoda yaushe.
»» UWATA ta kawo mana kwararren mai dafa mana ABINCI, domin muci me kyau musha me kyau.
»» UWATA tana kaimu gidan wasanni idan mundawo daga makaranta, domin
mushakata.
••• Lallaikam UWATA tacika mai ArZiKI..
~~~Nan take sai wata 'yar talaka ta mike tace mata ke saurara dalla kiji.
»» Ni UWATA dakanta muke takowa tarakomu
makaranta, saboda kar wani abu ya samemu.
»» UWATA itace take dafa mana
abinci da HaNNUNTA, kuma muma tana koya mana saboda GABA idan anyi mana Aure.
»» UWATA itace wacce bata cin Abinci har saimun Qoshi.
»» UWATA itace wacce take bamu GURASA da miya, ita kuma taci GAYA.
»» UWATA itace wacce take tsaremu agida tabamu tarbiyya.
Lallaikam UWATA itace uwa tagari mai kaunar YAYANTA.
Mala'ika JIBRILU (A.S) yayi ADDU'A yace:
Duk wanda yarayu da iyayensa har suka bar DUNIYA bai sami AL-JANNAH a karkashinsu ba, to ALLAH YAKIFAR DA
FUSKARSA ACIKIN WUTA...
Sai Annabi (S.A.W) yace:
AMEEN
Ya Allah kabamu ikon yimusu biyayya akan abinda kayi
TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A) 7.
TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A).
««kashi na 7»»
GUDUN MAWARSA GA ADDININ MUSULUNCI (2).
A lokacin da yawan musulmai yakai mutum tamanin da uku 83 sai Abubakar yanemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama dasu fito fili suyi kira zuwa ga Tafarkin Tsira wato Addinin Musulunci.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya Ankarar dashi irin hatsarin dayake tattare da daukar wannan mataki A dai-dai wannan lokaci, amma sai Abubakar yanace akan cewa mu gwada sa’armu.
Hakan kuwa akayi.
To, ammafa babu wanda yabiya harajin wannan kasada saishi Abubakar din.
Yanzu ya kuke gani mutum 83 sun fito suyi gwagwarmaya da duniya baki daya.
Ko iya wannan ya isa a gane girman Musulunci da kariya da UBANGIJI (S.W.T) yake bashi, domin addinin nasane.
Ai kuwa fitowar su keda wuya, da suka isa masallaci sai Abubakar yatashi domin ya gabatar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga mutane.
Ai kuwa basu bari yarufe bakinsa ba sai sukayi 'caa' akan Musulmi acikin masallaci mai alfarma.
Nan take kuwa suka tarwatsa taron musulmi.
Sannan suka farwa Abubakar da duka har saida suka kaishi Qasa ya fadi.
Sannan Utbatu dan Rabi’ata ya haye kan cikinsa yana amfani da takalman dake Qafarsa wajen dukan fuskar Saiyyiduna Abubakar (R.A).
Bai gushe ba yanayi masa duka har saida hankalinsa ya gushe, fuskarsa tayi jina-jina har ba a iya banbanta hancinsa da bakinsa.
Qabilar Abubakar ta Banu Taimin sunyo ciri domin su ceci dan uwansu.
Amma koda sukazo gayya ta gama aiki, mushrikai sun yi ta’adin da suke so akan Abubakar.
Sai suka daukeshi a halin yana cikin suma suna tsammanin ya mutu suka kuma lashi takobin idan har ya mutu zasu kashe Utbatu dan Rabi’ata abinda kuwa daya faru babu shakka zai haifar da wani gagarumin yaqi a tsakanin Quraishawa.
Amma sai Allah ya kiyaye, Abubakar ya farfado can a cikin dare.
Kalma ta farko kuwa data fito daga bakinsa itace:
Ina Manzon Allah ?
Kunji masoya Annabi na haqiqa.
Laifin dadi Qarewa.
Zanci gaba daga inda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Allah kabamu Albarkacinsu kasa muyi koyi dasu.
KADAN DAGA CIKIN DARAJOJIN KALMAR SHAHADA.
KADAN DAGA CIKIN DARAJOJIN KALMAR SHAHADA.
Wata rana wani mutum yashiga motar kasuwa zasuje LAGOS daga garin KAMBA
Bayan yashiga mota ya zauna sai ya tambaya ina driver yazo sutafi sai akace masa ai motar bata cikaba anajiran mutum biyu.
Sai yace agayama driver yazo sutafi mutumin yabiya kudin ragowar kujerar mutum biyu da basu zoba Yace yakamata motar ta tashi domin mutane suna sauri.
Bayan mutumin yabiya kudin sai sai daya daga cikin fasinjan dake cikin motar wani INYAMURI wato IGBO wanda ba musulmiba yace:
Gaskiya wannan mutum ya burgeshi daya biya wannan kudin don haka sakamakon wannan sadakar shi zai MUSULUNTA.
Wato addinin MUSULUNCI ya burgeshi yayi imani da ALLAH da MAZONSA (S.A.W).
Sai aka biya masa kalmar shahada daga nan yazama musulmi.
Bayan mota takama hanya dasu zuwa lagos
kwatsam sai motar tafadi dasu sukayi ACCIDENT.
ALLAHU AKBAR
Duk mutanen dake cikin motar ba wanda yayi komai sai sai wannan mutumin daya musulunta shine kawai ya mutu.
Tabbas Wannan mutumin yasami karshe mai kyau.
Ya ALLAH kayi mana kyakykyawan karshe.
ALLAH kasa mucika da kalmar "LAA ILAHA ILALLAHU MUHAMMADU RASULULLAH"
Domin alfarmar shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W).
Thursday, 11 January 2018
TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A) 7.
TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A).
««kashi na 7»»
TAIMAKONSA GA BAYIN ALLAH NAGARI.
Abubakar (R.A) yayi amfani da dukiyarsa wajen sayen bayi talakawa wadanda ake azabtar dasu akan Musulunci kamar irinsu:
1- Amiru dan Fuhairata wanda yake yahada uwa da 'yarsa Nana A'ishah.
Abubakar ya sayeshi daga hannun Dufail Bn abdullahi Bn Haris wanda yake azabtar dashi.
Sannan Abubakar ya 'yantashi, yasamu damar yin addininsa harma ya halarci yaqe-yaqen Badar da Uhud.
Yasami shahada a yaqin Mu'unah.
2- Sannan sai Bilal Dan Abu Rabah (Ladanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama).
Abubakar ya sameshi ana azabtar dashi saiya sayeshi daga mai gidansa Umayyatu dan Khalaf, ya 'yantashi.
Shima kuma ya halarci yaqe-yaqen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
3- Sannan sai Zinnirah, wata baiwar Allah da Umar dan Khaddab ya mallaketa kafin musuluntarsa, ya dinga azabtar da ita harsai data rasa idanunta, Sannan sai Mushrikai sukace, Lata da Uzza sun la'anceta shiyasa ta makance.
Amma imaninta da Allah yasa Madaukakin Sarki ya mayar mata da ganinta, sai sukace:
Wannan yana cikin sihirin Manzon Allah.
Akan wannan
baiwar Allah da izgilin da mushrikai keyiwa Musulunci akanta aya ta shadaya cikin suratul Ahqaf ta sauka.
Abubakar yafitar da ita daga Qangin bauta don ta samu 'yanci da bayar da tata gudunmawar ga addinin Allah.
Ba iya wadannan bayin Allah kadai Abubakar ya siya ya 'yanta su saboda Allah ba, akwai wasu bayi daga Qabilun Banu Adiyyin da Banu Abdi Shamsin suma sun mori karamcin Abubakar da kishinsa ga addini wajen samun wannan babbar gara6asar da yake neman yardar Allah da Manzonsa a kanta.
Laifin dadi Qarewa.
Zanci gaba daga inda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Allah kabamu Albarkacinsu kasa muyi koyi dasu.
INA MAZA DA MATA WADANDA SUKA SAMI MATSALAR IDO TA SANADIN WASA DA FARJINSU ???
INA MAZA DA MATA WADANDA SUKA SAMI MATSALAR IDO TA SANADIN WASA DA FARJINSU ???
Wannan abu shine ake kira "ISTIMNA'I" ko kuma "MASTURBATION" a turance.
Shine Mutum yadinga wasa da gabansa har maniyyi yakawo mace ko namiji hakan yanada illa sosai ga lafiyar jiki.
Sannan koda aure Akayi baza Aji dadinsa yadda ake buqata ba.
Wannan abu yana haifar da cututtuka samada guda 30 kwanakin baya nakawo bayanai akan yadda ake magance matsaloli guda 6 da wannan mummunar dabi'ar ke haifarwa.
Gasu kamar haka:
1. Yawan ciwan kai.
2. Rashin bacci.
3. Toshewar basira.
4. Yawan baqin ciki.
5. Rashin kaurin maniyyi.
6. Qanqancewar Gaba.
Yau kuma da yardar Allah zanyi bayani akan yadda za'a magance matsalar rashin gani sosai da wannan cuta ke haifarwa.
Wanda yake fama da wannan matsala saiya samo sassaken "Baure" ba ganyensa ba.
Saiya zubashi a tukunya yabashi wuta sosai harsai ya bararraka saiya saukeshi daga kan wuta, yasami wani dan mayafi haka ya lullu6a saiya bude tukunyar sannan yabude idonsa wannan tururin shi akeso yadinga shiga cikin idon.
Na rubutane saboda akwai wadanda suka tuba suna neman magani amma basu samuba.
IRIN BALA'IN DAKE TUNKAROMU A YANZU.
IRIN BALA'IN DAKE TUNKAROMU A YANZU.
TUNATARDA MUTANE TASHIN QIYAMA.
Zakaga Mutanen gari idan aka kawo musu hari kowa yana gudu, baya tuna matarsa ko 'ya'yansa ko 'yanuwansa kai harma iyayensa, suma haka, kowa takansa yake, wanima ruwa zai fada yamutu.
HMMM! to fa wannan aduniya kenan!
Kana iya gudu daga wata jiha zuwa wata jiha, daga 9jry zuwa Kamaru ko Chadi ko Nijar, to idan kiyama tazo to babu wurin gudu tunda zata game ko ina.
Babu sansanin 'yan gudun hijira! senatoci da 'yan majalisu na jiha da tarayya da ministoci da komishinoni da gomnoni da shuwagabannin kasashe duk ya rutsa dasu WALLAHI!
{Mutum zai gujewa dan'uwansa da mamarsa babansa da matarsa da 'ya'yansa, kowa sha'anin gabansa ya isheshi}
SURATU ABASA=34-37>
{mutum zaice ina wurin gudu ?
Sai ace a'ah babu mafaka"
<QIYAMA=10,11>
YAWAITA FASINJOJIN ALJANNAH.
Duk wanda Khawarijawa suka kasheshi muddin musulmine shi mai tauhidi to shine mafi alhairin gawa awurin ALLAH, kuma dan ALJANNA ne, inji FARIN JAKADA ANNABI (S.A.W).
WARE FASINJOJIN WUTA.
Duk azzalumi mai kashe mutane da gangan dan wutane dawwamamme.
<SURATUN NISA'I=93>
ANNABI (S.A.W) yakira Khawarij da karnukan wuta Acikin {SUNAN IBN MAJAH}
Ya Allah Ka daukaka Addinin Musulunci Da Musulmai.
Kuce "AMEEN" dan soyayyarku ga Muhammad Rasulullah.
BABAR ILLAR WASA DA FARJI KO AZZAKARI GA SAMARI DA 'YAN MATA MARASA AURE.
Assalam malam don Allah kataimakeni.
Na kasance ina wasa da gabana harnayi maniyi yanzu gashi ina fama da Matsaloli daban daban.
{1}. Rashin fahimtar komai
{2}. Rashin barci mai kyau.
{3}. Rashin kwanciyar hankali, ga ciwon kai, ga bacin rai, yau kimanin shekara biyar kenan naje asibiti nakashe kudi samada dubu hamsin ₦50,000 wajen test da sauransu.
Don Allah malam menene mafita ?
Don Allah aboye SUNANA.
AMSA
******
Da farko dai sai muce
INNA LILLAHIWA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
Wannan bawan Allah kagamu da babban bala'i.
Abinda ya Qara tayar min da hankali shine:
Ayau dinnan wasiku uku muka samu daga mutane daban daban, dukkansu masu irin wannan matsalar.
Harma akwai wadanda sukace su sun tubane ta sanadiyyar ziyartar wannan shafin namu da kuma karanta abubuwan da muke rubutawa.
Kwanakin baya lokacin da mukayi posting akan bayanin illolin da wannan mummunar dabi'ar take haifarwa, saida aka samu wasu shaidanu suna musantawa suna Qaryatamu.
Har suna cewa wai suma likitocin zamani ne.
To shin akwai wani likitan da yakai MANZON ALLAH (SAW)_?
Duk abinda kaji addini ya hanemu to lallai akwai wata illa mai girma acikinsa ne.
MAGANI INSHA ALLAHU
------------------------
Magani na farko shine kaje ayi maka RUQYAH.
Domin kuwa akan samu shaytanu wadanda suke makobtaka da mutum su shiga jikinsa a sanadiyyar wannan mummunar dabi'ar.
2. Sannan ka samu 'ya'yan tafasa ka dafasu kamar shayi karika sha da zuma INSHA ALLAHU jikinka zai dawo normal, zaka rika samun barci sosai.
3. ka samu ganyen NA'A-NA'A danye wanda bai gama bushewa ba, saika dafa shi kamar shayi, idan ya dahu saika tacheshi sannan ka zuba MAN-HULBA chokali daya aciki kasha ba tareda madara ba.
Kayi haka har sati 3.
INSHA ALLAHU basirarka zata bude.
Akwai bukatar duk wanda yake fama da irin wannan matsalar, indai yana bukatar samun waraka cikin gaggawa, toya yawaita ISTIGHFARI da salatin ANNABI (saw) domin su mabudaine na samun lafiyar ruhi da izinin Allah.
WALLAHU A'ALAM.
…………………………………………
WANI HADISI MAI TSORATARWA GA MUTANEN WANNAN ZAMANI.
WANI HADISI MAI TSORATARWA GA MUTANEN WANNAN ZAMANI.
An kar6o Daga uwar Muminai Nana Aishat (R.A) tace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:
Bayin da Allah yafi Qi Sune Wadanda Tufafinsu Yafi alkhairi (wato yafi kyau) fiye da aikinsu.
Sun kasance suna sanya kaya irin na Annabawa, (wato masu tsafta), Amma Aikinsu irin na masu girman kai.
Abinda ake nufi anan bawai kada mutum yayi kwalliya ba, a'a yayi duk irin yadda yakeso, amma yadinga tsayawa yagyara ibadarsa kamar yadda yake gyara kayansa ya6ata lokacinsa yasa musu bula ko sitati sudauki guga, haka akeso yagyara ibadarsa, amma sai kaga mutum yasha danyar shadda amma sallarsa bata wuce minti 1 zuwa 2.
Da fatan zamu kiyaye.
Ya Allah Ka Sanya Tsoronka A Zukatanmu.
AKAN WADANDA ZA A TASHI ALKIYAMA.
AKAN WADANDA ZA A TASHI ALKIYAMA.
Manzon Allah (S.A.W) yace:
Baza a tashi alkiyama ba, sai akan ashararen mutane, kuma Annabi (S.A.W) yace:
Ba za a tashi alkiyama ba sai anrasa wanda zaice 'ALLAHU ALLAHU' a bayan kasa.
Muslim ne ya ruwaito.
A cikin wani hadisin na Muslim Annabi (S.A.W) yace:
Zaa aiko wata iska mai taushi daga yaman, tafi Alharini taushi.
Ita wannan iska bazata bar wani mutum wanda akwai imani gwargwadon kwayan zarra a cikin zuciyarsa ba, face sai ta zare ransa.
Muslim ne ya rawaito shi.
To idan wannan iska ta dauke rayukan duk wani mai imani, to sai yarage babu kowa a bayan kasa sai kafiri dan kafura, sai mazinaci dan mazinaciya, za'a rufe Qofar tuba a lokacin, to akan wadannan ne za a busa kahon alkiyama.
(Wal iyazu billah).
Allahu Akbar.
Ya Allah kada kasa mukai wannan lokaci.
Allah ka albarkaci rayuwarmu.
NASIHA ZUWA GA SAMARI.
NASIHA ZUWA GA SAMARI.
====================
Hausawa nacewa gyara kayanka baya zama sauke muraba.
Wai yanzu ace saboda Allah 'ya'yan musulmaine ke irin wannan shigar, kash amma dai Allah wadaran naka ya lalace.
Wai har wani irin aski sukeyi wai shi "balatolly" .
Da kuma wani shegen wando mai suna suwaga ko kuma wizzy.
To iyaye kalubale agareku kusan cewa Allah zai tambayeku amanar daya baku.
Sannan mu samari ya kamata muyi karatun ta nutsu musanifa mune ababan alfahari awajen iyayenmu nan gaba, bai kamata mudinga koyi da turawa kafirai maciya amanar musulunci mubiye musu suna gurbata mana rayuwa ba.
Don Allah mukiyaye muji tsoron Allah (s.w.t)
Allah ya shiryemu gaba daya.
Mene shawara ga mace da bata san namiji ba ta rika tura yatsanta a farjinta dan ta rage sha,awa ?
Salam meye shawara ga mace da bata san namiji ba ta rika tura yatsar ta a farjinta dan ta rage sha,awa ?
m, malam dan Allah meye shawara ga mace da bata san namiji ba ta rika tura yatsar ta a farjinta dan ta rage sha,awa ?
(Daga Ambar Kabir)
AMSA
*****
Shawara agareta shine:
TAJI TSORON ALLAH TA DAINA AIKATA WANNAN MUMMUNAN FASADIN DOMIN KUWA ZATA MUTU TA ISKE DUKKAN ABINDA TA AIKATA.
Sannan tarage buri tayi aure. indai tana da manemi mai addini, koda mai mata uku ne gara ta amince masa ya turo manyansa ayi maganar aure, agaggauta kaita dakin mijinta.
Irin wannan abin shima FASADI NE kuma wani nau'ine na zina.
Munsha kawo hadisai ingantattu wadanda sukayi magana akan wannan mumunar dabi'a wacce ta watsu atsakanin maza da mata.
MANZON ALLAH (S.A.W) YA LISSAFA MASU YIN IRIN WANNAN DABI'A DAGA CIKIN MUTUM BAKWAI WADANDA ZASU HADU DA FUSHIN ALLAH, KUMA ALLAH BAZAI DUBESU DA RAHAMA ARANAR ALQIYAMA BA.
Duk matar da takeyin irin wannan mumunar dabi'ar zata iya haduwa da manyan illoli kamar haka:
{1}. ASARAR BUDURCINTA DA MATUNCINTA. Duk namijin daya aureta kuma yajita a haka, to tabbas zai gane cewar ita daman 'yar iska ce, kuma ba budurwa bace.
{2}. CHUTAR KWAKWALWA:
zata hadu da muguwar mantuwa da shakku acikin harkokin ibada.
{3}. CHIWON BAYA MAI WUYAR MAGANI
{4}. BARKEWAR JINI DA KUMA RIKICIN JININ AL'ADA.
YA ALLAH KA SHIRYI DUK MASU AIKATA IRIN WANNAN MUMUNAR DABI'AR MAZA DA MATA.
WALLAHU A'ALAM.
««WATA MUHIMMIYAR NASIHA ZUWAGA 'YAN UWANA MATA»»
««WATA MUHIMMIYAR NASIHA ZUWAGA 'YAN UWANA MATA»»
Assalamu Alaikum
Yaku 'Yan uwana Mata inaso in dan ja hankalinku da wata 'yar nasiha me Fa'ida,a kowanne lokaci ana alfahari daku domin kune kashin bayan tarbiyyar al'umma.
A wannan zamani mun tsinci kanmu cikin wani hali sabon Allah,Zinace-zinace da Alfasha sun yawaita, Don haka akwai bukatuwa ta ku kara sa'ido akan 'ya'yanmu Musamman mata, dukkan abun da yake dauke da fuskar rusa tarbiyyarsu ku kauce masa.
Kamar turasu zuwa tallace-tallace,da kuma Sa'ido akan tafiyarsu Makaranta da dawowarsu saboda ana samun report dayawa a makarantunmu idan antura yara makaranta sai su canja hanya,a samu wasu lalatattun samari suyi ta aikata lalata dasu.
Ya kamata kowacce uwa ta san irin kawayen da 'yarta take tare dasu domin dayawa kulla kawance da lalatattun kawaye yana rusa tarbiyyar yaranmu, kasancewar abokanan ko kawayen bazasu gusheba suna yimata hudubar shedan har sai sunga irin abunda suke aikatawa itama tana aikatawa.
Yana da kyau koda 'yarki tana zuwa makaranta ki zaunar da ita kina nuna mata kaza Haramunne ta gujeshi, kaza baida kyau kar tayi shi,kaza da kaza ya halasta agareta.
wannan shi zai sa ta tashi cikin tarbiyya me kyau, kuma ba iya nanba ki ka saka 'ya'yanki acikin addu'o inki Allah ya shiryar mana dasu.
Ki nuna mata haqqinki akanta, haqqin mahaifinta akanta, haqqin 'yan uwanta akanta, haqqin makobta akanta, Haqqin da yafi kowanne hakki akanta shine HAQQIN ALLAH SWT ki sanar da ita Dukkan wani hukunce-hukuncen da Allah ya ratayashi akanku mata.
Sannan akula dayin dinkin banxa domin Allah yayi tsinuwa ga masu baiyana tsiraici.
ILLAR DINKIN BANZA.
Illolin dake cikin dinkin banza suna da yawa, domin yana daga cikin illar dinkin banza tayar da sha awar mutane.
Wani na iya ganin dinkin dawata tayi yaga wani abu ajikinta sha awar sa ta tashi wanda kuma haka na iya kaishi ga aikata zina, kaga
dinkin banza na yada fasadi a bayan kasa, sannan da yada zinace zinace a tsakanin Al'umma.
kuma aduk lokacin da zinace zinace sukai yawa acikin mutane to rushewar wannan al'ummar ya yi saidai ajira lokaci, zakaga amfada cikin bala'e bala'e, masifu da cututtukan da ba a san kansuba ba sujin magani.
Yawan ganin tsaraici shikansa yana daga cikin abubuwan dasuke rushe tarbiyyar al'umma gaba dayanta.
KADAN DAGA DINKUNAN DA AKE YAYI YANZU.
1. FARALAYS:
Shine wanda za ayi hannu daya yafi daya, daya dogo daya gajere kokuma kasan riga a shanye gefe daya yafi
daya.
2. ZUGE DARLING:
Shine wanda ake masa wata igiya a kirji wanda za a zugeshi zam.
3. FITTED GOWN:
Itace rigar da ake matseta daga kasa har zuwa guiwa ta fitar da siffar wadda tasa ta daga sama har zuwa guiwa idan anzo guiwa sai abude ta.
4. HIGH WAIST:
Itace wacce a ke mata sket dogo sai asa rigar kanti asama mai karamin
hannuu ko babban hannu.
5. JAHANNAMA GA FASINJA.
6. SHOW ME YOUR BACK (NUNA MIN BAYANKI).
7. BREAST CURVE (MAI RIGAR NONO).
8. KEREWA da dai sauransu.
MEYE ZAI HANA DINKIN BANZA?
Abinda zai hana dinkin banza shine jin
tsoron Allah, ganin girmansa da kuma sanin
muhimmancin koyi da karantarwar Manzo
Allah (S.A.W).
Teloli suji tsoron Allah subada suma tasu gudun mawar wajen umarni da kyakykyawan aiki da hani ga mummunan aiki.
mukoma ga addini gaba ki daya bawai addini a masallaci ko makaranta kawai ba, mubar koyi da yahudu da nasara
kan wannan rayuwar duniyar mai ka rewa.
Mu yarda dacewa ba wata wayewa inba wayewar addinin musulunci ba.
Allah yabamu ikon gyarawa.
Wassalamu alaikum wara hamatullah.