KAYI KOMAI BA KOMAI AL-JANNAH TA MAI RABO CE:
Mene ne ingancin wannan maganar?
A haqiqanin gaskiya muna wasa da Allah, ta inda muke furtawa da harsunanmu abubuwan da ke fusata Ubangiji, kuma muna sane muke yin haka.
Amma da yake Allah Ta'ala mai rahma ne sai yake qyalemu baya azabtar damu da zarar mun furta munanan kalmomi, sai yabamu lokaci har mu tuba.
Amma wannan bai kamata yazame mana hujjar cigaba da furuci barkatai ba, ya zamana duk abinda muka gadama kawai sai mu furta.
Babu yadda za'ayi wanda yasan daraja da qimar addini ya furta wannan kalma, saboda muninta.
Amma baya wuce dayan biyu:
1. Imma dai jahilci:
Saidai jahilci baya iya zama hujja ga bawa, dolene bawa yayi Ilmin sanin Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Addininsa.
2. Ko kuma tashen balaga da rud'in shaid'an.
'Dan'uwa ka auna wad'annan kalmomi domin gano munin su:
Ka yi komai ba komai aljannah ta mai raboce.
Ma'ana:
Ka aikata duk abinda kakeso ko mene ne kuma komai muninsa a wurin Allah.
Misali:
Ka yi zina
kayi luwad'i.
ko kiyi madigo
kayi qarya.
kayi caca.
kaci riba.
kaci haram.
ka yi kisan kai.
kasha giya da sauransu.
ka aikata duk wani nau'in aiki da kakeso komai muninsa, kada kaji komai ai aljannah ta mai raboce.
(Wal'iyadhu Billah).
Wannan fa shine irin munin da wadannan kalmomi ke qunshe dasu.
Da yawan masu furta wadannan kalmomi sune 'yan uwanmu matasa 'yan bana-bakwai, wadanda gigin balaga ke dibarsu, da kuma 'yan mata wad'anda kejin kansu ta fuskar sha'awa kuma babu tarbiyya, sai wasu daga cikin zaurawa wadanda basu kwankwadi tarbiyya ba.
Shiyasa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana mana a cikin hadithi cewa:
(( Mafi yawan abubuwan da ke kai mutane wuta shine furucin harsunansu.
Don haka mu kiyayi Allah, mu daina furta kalmomi barkatai wad'anda bamu san ma'anonin su ba, saboda gudun furta kalmar dake fusata Ubangiji, saboda haka mu dinga sanin kalmomin da zamu dinga furtawa, domin kaucewa afkawa halaka.
***************************
Allah ya shiryar da mu akan hanya madaidaiciya, ya yafe mana kusa-kuranmu wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba, ya kuma tsare mu daga afkawa halaka.