Sunday, 14 January 2018

MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI ???

Tags

MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI ???

AMSA
-----
Zakkar fidda kai sunnah ce daga cikin sunnar Manzon Allah (S.A.W).

Manzon Allah da kansa ya aikata ta, hakama sahabbansa sun aikakata.

Za'a iya fidda ita kafin ganin wata, domin sahabbai sun aikata haka.

Ana fitar da zakkar fidda kai ga kowane musulmi, yaro da babba, mace da namiji, 'Da ko kuma bawa, kowane mutum mudun nabi hudu.

Amma abin mamaki mafi yawan mutane basu damu da fitar da itaba, saboda da'awar talauci.

HAKIMAR ZAKKAR FIDDA KAI

TSARKAKE MAI AZUMI:

Tana tsarkake mai azumi daga kuskuren daya aikata acikin azuminsa na ramadan kamar zantukan banza, zagi, kallon haram da sauransu.

SANYA WALWALA AZUKATAN 'YAN UWA MUSULMI:

Zakkar fidda kai tana sanya walwala a zukatan 'yan uwa musulmai ta yadda babu wani dan uwa da zai nemi abinci da zaici a ranar farin cikin sallah yarasa, da sauransu.

SUWA YA KAMATA SUYI ZAKKAR FIDDA KAI ???

Hakika zakkar fidda kai ta rataya akan dukkan musulmi mai 'yanci ko bawa, babba ko yaro, namiji ko mace.

TAMBAYA ???

SHIN YA TABBATA WANDA BAI FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAIBA, ZA'A RATAYE AZUMINSA, BA ZA'A KARBA BA HARSAI RANAR DA YA BAYAR ???

AMSA

A'a Wannan hadisin bai tabbata daga bakin manzon Allah ba.

Hadisi ne mai rauni, kuma duk mutumin daya bari aka sauka daga idi bai bayar ba, hukuncin zakkarsa kamar sauran sadaka ne ba zakkar fidda kai bace.

WALLAHU A'ALAM

YA ALLAH KADATAR DAMU

Dan Allah kuyi Like da share dinsa saboda yan uwanku su amfana.

Allah ya hadamu acikin ladan baki daya.