TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A).
««kashi na 7»»
TAIMAKONSA GA BAYIN ALLAH NAGARI.
Abubakar (R.A) yayi amfani da dukiyarsa wajen sayen bayi talakawa wadanda ake azabtar dasu akan Musulunci kamar irinsu:
1- Amiru dan Fuhairata wanda yake yahada uwa da 'yarsa Nana A'ishah.
Abubakar ya sayeshi daga hannun Dufail Bn abdullahi Bn Haris wanda yake azabtar dashi.
Sannan Abubakar ya 'yantashi, yasamu damar yin addininsa harma ya halarci yaqe-yaqen Badar da Uhud.
Yasami shahada a yaqin Mu'unah.
2- Sannan sai Bilal Dan Abu Rabah (Ladanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama).
Abubakar ya sameshi ana azabtar dashi saiya sayeshi daga mai gidansa Umayyatu dan Khalaf, ya 'yantashi.
Shima kuma ya halarci yaqe-yaqen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
3- Sannan sai Zinnirah, wata baiwar Allah da Umar dan Khaddab ya mallaketa kafin musuluntarsa, ya dinga azabtar da ita harsai data rasa idanunta, Sannan sai Mushrikai sukace, Lata da Uzza sun la'anceta shiyasa ta makance.
Amma imaninta da Allah yasa Madaukakin Sarki ya mayar mata da ganinta, sai sukace:
Wannan yana cikin sihirin Manzon Allah.
Akan wannan
baiwar Allah da izgilin da mushrikai keyiwa Musulunci akanta aya ta shadaya cikin suratul Ahqaf ta sauka.
Abubakar yafitar da ita daga Qangin bauta don ta samu 'yanci da bayar da tata gudunmawar ga addinin Allah.
Ba iya wadannan bayin Allah kadai Abubakar ya siya ya 'yanta su saboda Allah ba, akwai wasu bayi daga Qabilun Banu Adiyyin da Banu Abdi Shamsin suma sun mori karamcin Abubakar da kishinsa ga addini wajen samun wannan babbar gara6asar da yake neman yardar Allah da Manzonsa a kanta.
Laifin dadi Qarewa.
Zanci gaba daga inda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Allah kabamu Albarkacinsu kasa muyi koyi dasu.