Sunday, 14 January 2018

SOYAYYA ITACE:

Tags

SOYAYYA ITACE:
Lokacin da Sahaby Bilal (r.a) yakasa zama a Madeena, bayan mutuwar Manzo (S.A.W)..!!!
-Domin duk sanda yafara kiran Sallah in yazo"ASH'HADU ANNA MUHAMMAD RASULULLAH" sai muryarsa ta shaqe saboda kuka....!!!
Sai yanemi iznin Khalifa Abubakar (r.a) yakoma SHAAM yahadu da wasu Sahabbai acan.....!!!
-Bai sakeyin kiran Sallah ba har saida yayi mafarki da masoyinsa (S.A.W) yace masa:
HABA BILAL WACE IRIN BUSHEWACE HAKA??
SHIN LOKACI BAI YIBA DAZAKA ZIYARCEMU??).
-Tuni Sahaby Bilal (ra) yadora siddin dokinsa sai madeena, yana shiga bai tsaya ko inaba sai masallacin Manzon Allah (S.A.W) yazauna gurin qabarin yanata kuka, harsai da jikokin Manzo (S.A.W) Hasan da Husain sukazo suka sameshi....!!!
Suka rungumeshi suna goge masa qasa a jikinsa...!!!
suka nemeshi Alfarma da yayi kiran Sallah...!!!
-Sahaby Bilal (r.a) yatashi ya hau minbari yafara:
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR 2...!!!
-ASH'HADU ANLA ILAHA ILLALLAH....!!!:
Tuni Madeena ta dauka da hayaniya da koke- koke....!!!
-yana fadin:
ASH'HADU ANNA MUHAMMADURRASULULLAH...
Shima sai kuka yaqwace masa!!!
Mutanen Madeena duk suka fiffitoi daga gidajensu....
BA'A TABA GANIN RANAR DA AKAYI KUKA BA IRINTA BA, TUN RANAR MUTUWAR MANZO SAW.....(A tarihi)
ALLAHUMMA SOLLI WASALLIM ALA NABIYYINA MUHAMMAD WA ALA AALIHI WASAHBIHI WASALLIM.

Domin samun darasi irin wannan akoda
yaushe ku ziyarci wannan shafi kamar haka.
…………………………………………
…………………………………………