Sunday, 22 April 2018

DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU.

Tags

DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU.

Manzon Allah (S.A.W) yace:

"Wanda ya karanta Alqur'ani yana cikin Sallah, ga kowane harafi yanada lada dari.

Kuma wanda ya karanta Alqur'ani ba cikin Sallah ba amma yana da alwalla, shi kuma ga kowane harafi yanada lada Ashirin da biyar.

Kuma wanda ya karanta Alqur'ani batare da alwalla ba, ga kowane harafi yanada lada goma".

Wannan hadisin akwaishi acikin MUJALISUL ANWAR da DURRATUN NASIHINA.

Allahu Akbar!

Alqur'ani babban kundi!

Gulbi kake ba'a kai gacinka!

Kowa ya rike ka yadace!

Gaka Haske! Gaka Shiriya!

Gaka Hanya mikakkiya har aljannah!

Allah Sarkin rahama !

Alqur'ani yanada harafi guda DUBU DARI UKKU DA ASHIRIN DA UKKU, DA DARI SHIDDA DA SABA'IN DA DAYA. (323,671).

Don haka ga yadda lissafin yake:

WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI CIKIN SALLAH.

Yana da lada: 32,367,100. Miliyan Talatin da biyu, da dubu dari ukku da sittin da bakwai da dari daya.

WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BA CIKIN SALLAH BA AMMA YANADA ALWALLA.

Yana da lada: 8,091,775. Miliyan takwas da dubu casa'in da daya da dari bakwai da saba'in da biyar.

WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BATARE DA ALWALLA BA.

Yana da lada: 3,236,710. Miliyan ukku da dubu dari biyu da talatin da shidda da dari bakwai da goma.

Don haka ya kamata ace kowane musulmi yana samun kashi guda daga cikin su, a kalla ya sauke Al-qur'ani sau daya duk bayan wata biyu.

Duk wanda baya karanta alqur'ani, to yanzu dai yaga irin hasarar ladar da yakeyi.

Shi kuma wanda yake karanta alqur'ani, to yaga dai irin ladan da yake samu.

Allah yakara sanya rabonmu a ciki, yakuma kara bamu ikon cigaba da karantawa.

www.tafarkintsira.wapka.me