TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A).
««kashi na 7»»
GUDUN MAWARSA GA ADDININ MUSULUNCI (2).
A lokacin da yawan musulmai yakai mutum tamanin da uku 83 sai Abubakar yanemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama dasu fito fili suyi kira zuwa ga Tafarkin Tsira wato Addinin Musulunci.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya Ankarar dashi irin hatsarin dayake tattare da daukar wannan mataki A dai-dai wannan lokaci, amma sai Abubakar yanace akan cewa mu gwada sa’armu.
Hakan kuwa akayi.
To, ammafa babu wanda yabiya harajin wannan kasada saishi Abubakar din.
Yanzu ya kuke gani mutum 83 sun fito suyi gwagwarmaya da duniya baki daya.
Ko iya wannan ya isa a gane girman Musulunci da kariya da UBANGIJI (S.W.T) yake bashi, domin addinin nasane.
Ai kuwa fitowar su keda wuya, da suka isa masallaci sai Abubakar yatashi domin ya gabatar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga mutane.
Ai kuwa basu bari yarufe bakinsa ba sai sukayi 'caa' akan Musulmi acikin masallaci mai alfarma.
Nan take kuwa suka tarwatsa taron musulmi.
Sannan suka farwa Abubakar da duka har saida suka kaishi Qasa ya fadi.
Sannan Utbatu dan Rabi’ata ya haye kan cikinsa yana amfani da takalman dake Qafarsa wajen dukan fuskar Saiyyiduna Abubakar (R.A).
Bai gushe ba yanayi masa duka har saida hankalinsa ya gushe, fuskarsa tayi jina-jina har ba a iya banbanta hancinsa da bakinsa.
Qabilar Abubakar ta Banu Taimin sunyo ciri domin su ceci dan uwansu.
Amma koda sukazo gayya ta gama aiki, mushrikai sun yi ta’adin da suke so akan Abubakar.
Sai suka daukeshi a halin yana cikin suma suna tsammanin ya mutu suka kuma lashi takobin idan har ya mutu zasu kashe Utbatu dan Rabi’ata abinda kuwa daya faru babu shakka zai haifar da wani gagarumin yaqi a tsakanin Quraishawa.
Amma sai Allah ya kiyaye, Abubakar ya farfado can a cikin dare.
Kalma ta farko kuwa data fito daga bakinsa itace:
Ina Manzon Allah ?
Kunji masoya Annabi na haqiqa.
Laifin dadi Qarewa.
Zanci gaba daga inda muka tsaya a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Allah kabamu Albarkacinsu kasa muyi koyi dasu.
Friday, 12 January 2018
TARIHIN SAYYIDUNA ABUBAKAR AS-SIDDIQ (R.A) 7.
Penulis tafarkintsira
Diterbitkan January 12, 2018
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)