Sunday, 22 April 2018

FIFIKON ANNABI (S.A.W) DA AL'UMMARSA AKAN SAURAN AL'UMMATAI.

Tags

FIFIKON ANNABI (S.A.W) DA AL'UMMARSA AKAN SAURAN AL'UMMATAI.

Lokacin da Allah ya kusantar da Annabi Musa (A.S) izuwa gareshi yayi zance dashi akan dutsen Sinaa' sai ya tambayi Allah cewa:

"Ya Ubangiji shin duk cikin bayinka kuwa, akwai wanda yafini girma awajenka ?

"Naga ka kusantar dani gareka, kuma gashi kanayin zance dani"

Sai Ubangiji yace masa:

"Na'am!

Annabi Muhammadu (S.A.W) yafika girma awajena".

Sai Annabi Musa (A.S) yasake cewa:
"To Ya Ubangiji, indai Annabi Muhammadu (S.A.W) yafini girma awajenka, to shin Al'ummarsa fa sunkai Banu Isra'eela girma awajenka?"

"Naga ka yanka musu teku sun ratsa ta cikinsa Ka tseratar dasu daga Fir'auna da Jama'arsa.

Sannan ka ciyar dasu daga Mannu da kuma Salwa."

Sai Ubangiji yace masa "Na'am.

Al'ummar Muhammadu (S.A.W) sunfi Banu Isra'ila girma awajena"

Sai Annabi Musa (A.S) yace:

"Ya Ubangiji inaso kanuna min Al'ummar Muhammadu (S.A.W) ingansu".

Sai Ubangiji yace masa:

"Ya Musa bazaka gansu ba, Saidai zan jiyar dakai sautinsu".

Sai yace:

"To ya Ilahee"

Sai Ubangiji yayi kira cewa:

"Yaku Al'ummar Muhammadu (S.A.W)! ku amsa kiran Ubangijinku!"
Sai suka amsa alhali sannan suna cikin tsatson iyayensu maza, da kuma mahaifun iyayensu mata har izuwa ranar Alkiyama.

Suka ce:

"MUN AMSA MAKA YA UBANGIJI!

TABBAS KAINE UBANGIJINMU DA GASKE.

KUMA MU BAYINKA NE DA GASKE".

Sai yace:

"KUNYI GASKIYA, TABBAS NINE UBANGIJINKU DA GASKE. KUMA KU BAYINA NE DA GASKE.

HAQIQA NAYI MUKU AFUWA (Na gafarta muku). KUMA NABAKU (FIFIKO) TUN KAFIN KU ROKENI.

"DUK WANDA YA SADU DANI DAGA CIKINKU YANA MAI SHAIDA CEWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, ZAI SHIGA ALJANNAH".

(Ibnu Mirdawaihi ne ya ruwaito daga Abdullahi bn Abbas (R.A).

Ya Allah kaqara tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W).