Sunday, 14 January 2018

INA SAMARI DA 'YAN MATA ???

Tags

INA SAMARI DA 'YAN MATA ???

Ku karanta wannan.

Lallai hadisai sun tabbata wadanda a cikin su Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake kwadaitar da mai neman aure yaje ya ga wadda yake nema, domin wannan shi zai janyo hankalinsa zuwa son ta har ta kaishi ga auren ta.

Daga ciki akwai hadisin da Abu Huraira radhiyallahu anhu yace:

"Na kasance tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sai wani mutum ya zo, ya ba shi labarin cewa ya auri wata mace daga cikin matan Madina.

Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:

“Shin kaje ka ganta?

”sai yace:

‘A’a ban jeba.

’Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace dashi;
Kaje ka ganta, saboda akwai wani abu a cikin idanun mutanen Madina.

Haka kuma hadisi ya tabbata daga Jabir Ibn Abdullahi radhiyallahu
anhu yace:

"Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace:

Duk wanda zai nemi auren mace daga cikinku.

idan ya samu ikon ya kalli abin da zai ja hankalinsa ga auren ta, toya aikata".

A bisa wadannan dalilai wasu malamai suke ganin cewa za a iya kallon duk wani sashe na jikinta wanda zai janyo hankalinsa ga auren ta, amma ban da al`aurarta.

Wannan shi ne abin da Imamul Auza’i ya fada.

Saidai mafi yawan malamai suna ganin cewa, abin da ya halatta a kalla kawai,
shine fuskarta da tafin hannunta, domin su ne suke nuna kyawun mace.

Kuma sun shardanta cewa;

Wannan kallon ya kasance don jan hankali
ne zuwa ga auren ta kawai, ba don janyo fitina da tayar da sha`awa ko faruwar fasikanci ba.

Haka kuma shari`ar Musulunci ta hana mai
neman aure kadaita da wadda yake nema a zaure ko daki ko falo ko kuma kadaita kowace irin nau’i ce.

Domin Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallam yace:

"Kada wani mutum ya kadaita da wata mace, kuma kada wata mace tayi tafiya, face tare da ita akwai muharraminta…

Sauda yawa zaka ga samari suna raka yan matansu bakin titi, da sunan wayewa!

To mu sani cewa kadaita, tana jawo fitina da waswasin shaidan.

Don haka, masu yin zance suyi hattara da kadaita da matan da suke so.

Yana daga cikin mummunar al`adar da ake aikatawa a wannan zamani yadda ake
yawaita zance kullum da surutai marasa fa`ida.

Haka kuma yana daga cikin dabi`un da basu kamata ba, yi wa mace alkawarin karya da nufin wai za a cika mata bayan aure.

Haka kuma akwai masu yin aron sutura ko abin hawa, yayin zuwa
zance don yaudara, duk wannan bai kamata ba.

Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu yace:

Manzon Allah (s.a.w) ya ce:

"Alamomin munafiki guda
uku ne!

1. Idan ya yi zance sai yayi karya.

2. Idan an bashi amana sai yayi ha`inci.

3. Idan yayi alkawari sai ya saba.

Saboda haka muna nasiha ga `yan’uwanmu mazaje dasu nisanci wadannan siffofin marasa kyau.

Haka kuma su ma `yan’uwanmu mata su ji tsoron Allah, domin babu abin da ke sa a yi musu karya da yaudara, sai kwadayi da son abin duniya.

Haka kuma yana daga cikin munanan al`adu a wannan zamani, yadda wasu ke kwaikwayon
al`adun Turawa na yin hannu da wadda suke so su aura, ko rike hannunta
da sauran abubuwan da
suke kai wa ga aikata alfasha da fasikanci.

Bayan kuwa hadisi ya tabbata daga Nana A’isha (R.A) tace:

Na rantse da Allah!

Hannun Manzon Allah (s.a.w) bai taba shafar hannun wata mace ba yayin mubaya’a, sai dai yana
mubaya’a da su ne ta hanyar maganayace:

Na karbi mubaya’arku.

Don haka idan har
Manzon Allah (s.a.w) da Allah ya aiko shi zuwa ga dukkan talikai, kuma yayi masa kariya daga aikata sabo ya guji wannan, don mene ne kai za ka fada cikin wannan
mummunan aiki alhali baka da wani abin koyi fiyeda Manzon Allah (s.a.w) ba.

Haka kuma yana daga cikin munanan dabi`u a wannan zamani, ta yadda
wasu masu neman aure suke wassafawa
abokansu kyawu da kuma siffofin macen da suke so su aura.

Idan kuma ba sa son ta ko
kuma an samu sabani a tsakaninsu, sai su rika aibata ta ga mutane kuma su rika tona
asirinta, haka su ma matan suke aikatawa.

Kai! Abin ma har ya kai a tsakaninsu suna aikawa juna munanan sakwanni da hotuna na batsa ta hanyar wasika a waya (text message) da yanar
gizo-gizo (Internet), ta
yadda za ka ga `ya`yan musulmi suna aikawa da hotunansu tsirara a shafin Facebook da Twitter da 2go da sauransu, Wa
Iyazu Billah!

Wannan abu
ya kai matukar muni dalalacewar tarbiyya.

To, a nan ina so a
fahimci cewa; tushen mafi yawan matsalolin da
muka ambata, suna faruwa ne daga iyaye, saboda sakacinsu ga sha`anin tarbiyyar `ya`yansu wanda yake kai su ga nadama lokacin da
nadamar ba za ta yi amfani ba.

Nasiha ta ga `yan’uwa mata kuma ita ce: su ji tsoron Allah, su rike addininsu da mutuncin gidajensu, kada don suna jin wayewar kai, ko kiraye- kirayen Turawan yamma na `yancin mata ko zurfin ilimin zamani, ya sa mace ta zubar da
mutuncinta ko ta bayar da kanta ga wanda ba mijinta ba.

Domin wannan zai kai tane kawai zuwa ga halaka.

Da fatan zamuyi aiki da wannan nasih.