Sunday, 14 January 2018

MU'UJIZA MAI GIRMA.

Tags

MU'UJIZA MAI GIRMA.
----------------------------
Wata rana akusa da Khaibar (wani garin yahudawa ne).

Manzon Allah (s.a.w) ya kwanta, ya 'dora Kayinsa abisa Qafafun Sayyiduna Aliyyu (r.a) alhalin ana saukar masa da WAHAYI adaidai lokacin.

Har akayi La'asar amma shi Sayyiduna Aliyyu bai yiba.

Har rana tafadi sannan Manzon Allah (s.a.w) ya farka.

(Wahayin ya idda sauka).

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya tambayeshi cewa:

"YA ALIYYU shin kayi sallar la'asar ne ?"

Sai yace "A'a banyi ba YA RASULALLAH.

(Alhali rana ta riga tafadi).

Nan take sai Manzon Allah (s.a.w) yacira hannuwansa masu Albarka, ya roki Allah yana cewa:

"YA UBANGIJI!!

ALIYYU YA SHAGALTU NE ACIKIN BIYAYYARKA DA BIYAYYAR MANZONKA.

DON HAKA (YA ALLAH) KA MAIDO MASA DA RANA (domin yayi sallah)."

Sayyidah Asma'u (wacce ta ruwaito hadisin) tace:

"Tun da farko mun ga lokacin da rana tafadi.

Amma Wallahi nan-da-dan sai muka ganta ta dawo da baya, ga haskenta nan a doron Qasa da duwatsu"

ALLAHU AKBAR!!!

Kunji fa!

Ranar ta dawo da baya har Manzon Allah (s.a.w) da Sayyiduna Aliyyu (r.a) sukayi sallarsu suka idar.

Sannan ta sake komawa ta fadi.

Duk wanda yayi kokwanta akan mu'ujizar Annabi, imaninsa mai rauni ne.

Ibnu Katheer ne yakawo wannan hadisin acikin ALBIDAYAH WAN-NIHAYAH juzu'I na 6 shafi na 80, 81, da kuma na 85.

Sannan aduba TAFSEER na Imamul Qurtubiy juzu'I na 5 shafi na 97.

Allah kaqara mana Soyayya Muhammad Rasulullah.