KUCI ANAN MUNCI ACAN:
.
ANYA WANNAN MAGANAR GASKIYA CE KUWA ?
.
A yayin daka tsinci kanka cikin wadata to, kada kayi tinqaho da fankama gamida toroqoqo tare da yiwa sauran mutane kallon hadarin kaji.
Wannan duniya ba komai bace, shiyasa zakaga Allah yana bawa kowa ita, sabanin lahira.
Babu wanda yake samun ta face mumini.
Hatta a watan azumi, akwai wanda yake sahur da buda baki da kala-kalan abinci na gani da fada, sakamakon wadatar dukiya da Allah ya bashi, yayin da zakaga wani wallahi da sauran tuwo ko ragowar kunu yake sahur, kuma yayi buda baki da qwayoyin dabino da kunu da qosai, haka zai yi haquri har zuwa asubahi kuma ya dauki wani azumin a hakan.
To, koma dai acikin wacce tawaga Allah ya jefaka, haka zaka bautawa Allah yadda ya cancanta ka shiga aljanna, haka kuma zaka keta alfarmar shari'a ka sabawa Allah ka shiga wuta.
(Wal'iyadhu Billah).
Akwai wata magana da malam bahaushe yakeyi wai: KUCI ANAN MACI ACAN!
Hmm wannan magana akwai gyara, ba sunnar Allah bace cewa duk wanda yaci anan ba zaici acan ba.
Kuma wanda bai ci anan ba zaici acan, wannan ba haka bane.
Zai iya yiwuwa:* kaci anan kuma kaci acan.
Ko kaci anan kuma baza kaci acan ba.
Ko kuma bakaci anan ba kaci acan.
Ko kuma bakaci anan ba kuma baza kaci acan ba.
(Wal'iyadhu Billah).
Ba alama ce ta rashin rabo a lahira ba don kasamu arziqi a duniya, ba kuma alama ce ta rabo a lahira ba don baka samu arziqi a duniya ba, kuma kasani zaka iya rayuwa cikin talauci da quncin rayuwa a duniya kuma ka shiga wuta a lahira.
Haka kuma zaka iya rayuwa cikin wadata da yalwar dukiya a duniya kuma ka shiga aljanna a lahira.
ko sabanin haka.
Talauci da wadata duk jarabawa ce Allah yake yiwa bayinsa a rayuwa.
Kada karudu da wannan magana ta malam bahaushe ka yaudari kanka cewa wai tunda baka samu arziqi a duniya ba to, a lahira kune 'yan aljanna!
"Hmmm sannu dan gata"
Wallahi zaka yaudari kanka, kaidai kaci gaba da bin dokokin mahaliccinka sauda-qafa, yi-nayi, bari-na bari, sannan ka qasqantar da kai a gareshi, wannan shine mafita kuma ita ce hanyargaskiya.
Idan bakabi Allah (S.W.T) ba, azaba zai maka, babu ruwansa da talaucinka.
*************************
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, yaqara mana imani da taqwa tareda qanqame shiriyar Manzon Allah.
(Sallallahu Alaihi Wasallam).