ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI :
1. Idan ya zamto baka jiran sallah saidai
sallah ta jiraka.
2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur'anin ka ba (wai bakada lokaci).
3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka sabawa ubangijinka.
4. Idan ya zamto kullum tunaninka yadda zakayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi.
5. Idan ya zamto baka karbar nasiha.
6. Idan ya zamto babu rayuwar da take
birgeka sai rayuwar mawaka da 'yan kwallo da makada.
7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa'azi ko karatun al-qur'ani.
8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheri sai watarana.
9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin addininka sai dai na neman duniya (boko).
10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon bai Qareka da komai ba.
Allah (swt) Ya yafe mana zunuban mu manya da qanana.
Manzon Allah (saw) yanacewa mutanen dake kusa dani a ranar tashin Alkiyama sune masu yawan yi min salati!
Ya Allah muna rokonka da sunayenka tsarkaka, don darajar Al'arshi, don girman mulkinka Allah, don soyayyar ka da Annabi Muhd (saw) duk wanda ya tura wannan sakon ga yan uwa musulmi koda mutum 5 ne ya Allah kaji kansa, ka gafar ta masa, ka daukakashi duniya da lahira, ka kareshi daga makiya, ka hadashi da manzon Allah (saw) ranar alkiyama sannan ka sakashi Aljanna Firdausi