YADDA AKE WARWARE SIHIRI.
TAMBAYA:
Assalamu alaikum.
Dan Allah malam a fitar dani daga cikin duhu gameda abin da yake damuna.
Mahaifiya tace taje gurin Boka ayi mata naganin ciwon mara da yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara guda da rabi, amma likitoci sunyi scanning sunce ba komai tosai Bokan yace mata asiri akayi mata, kuma zaiyi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma zata kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata bata aminta da Bokan bane.
Shiyasa Nakeso kabani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini ?
Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita ?
Wassalam nagode malam Allah yaqara basira.
(Daga Binta Umar).
AMSA
-----
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, tabbas ba'a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani.
Wasu malaman sunyi bayani cewa:
Ana iya warware sihiri ta hanyar karanta wadannan ayoyi kamar haka:
1- Ayatul-Kursiyyu.
2- Quliya.
3- Ikhlas.
4- Falaki da Nasi.
5- Sai kuma ayah ta: 117 zuwata 122, cikin Suratul A’araf.
6- Sai kuma Ayah ta: 79-81 cikin Suratu Yunus.
7- Sannan sai Ayah ta: 65-70 cikin Suratu Dhaha.
Za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka dashi a waje mai tsafta.
Haka ake magance sihiri cikin yardar Allah.
Bai halatta ki taimaka mataba, wajan bada wadannan kayan da boka yanema duk da cewa mahaifiyarkice.
Saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.
Ya wajabta gareki kayi mata nasiha cikin hikima, kisanar da ita cewa:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
“Duk wanda yaje wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah bazai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in”
Muslim ya rawaito acikin hadisi mai lamba ta: 2230.
Kinga idan mutum ya mutu acikin wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita.
Sannan awani hadisin kuma yana cewa:
“Duk wanda yaje wajan boka ya gaskata abin daya fada, to tabbas ya kafurce da abinda Annabi Muhammad yazo dashi”
Kuduba Sunanu-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta: 3904, kuma Albani ya inganta shi.
INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZAKI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.
Allah Shine mafi sani.