««WATA MUHIMMIYAR NASIHA ZUWAGA 'YAN UWANA MATA»»
Assalamu Alaikum
Yaku 'Yan uwana Mata inaso in dan ja hankalinku da wata 'yar nasiha me Fa'ida,a kowanne lokaci ana alfahari daku domin kune kashin bayan tarbiyyar al'umma.
A wannan zamani mun tsinci kanmu cikin wani hali sabon Allah,Zinace-zinace da Alfasha sun yawaita, Don haka akwai bukatuwa ta ku kara sa'ido akan 'ya'yanmu Musamman mata, dukkan abun da yake dauke da fuskar rusa tarbiyyarsu ku kauce masa.
Kamar turasu zuwa tallace-tallace,da kuma Sa'ido akan tafiyarsu Makaranta da dawowarsu saboda ana samun report dayawa a makarantunmu idan antura yara makaranta sai su canja hanya,a samu wasu lalatattun samari suyi ta aikata lalata dasu.
Ya kamata kowacce uwa ta san irin kawayen da 'yarta take tare dasu domin dayawa kulla kawance da lalatattun kawaye yana rusa tarbiyyar yaranmu, kasancewar abokanan ko kawayen bazasu gusheba suna yimata hudubar shedan har sai sunga irin abunda suke aikatawa itama tana aikatawa.
Yana da kyau koda 'yarki tana zuwa makaranta ki zaunar da ita kina nuna mata kaza Haramunne ta gujeshi, kaza baida kyau kar tayi shi,kaza da kaza ya halasta agareta.
wannan shi zai sa ta tashi cikin tarbiyya me kyau, kuma ba iya nanba ki ka saka 'ya'yanki acikin addu'o inki Allah ya shiryar mana dasu.
Ki nuna mata haqqinki akanta, haqqin mahaifinta akanta, haqqin 'yan uwanta akanta, haqqin makobta akanta, Haqqin da yafi kowanne hakki akanta shine HAQQIN ALLAH SWT ki sanar da ita Dukkan wani hukunce-hukuncen da Allah ya ratayashi akanku mata.
Sannan akula dayin dinkin banxa domin Allah yayi tsinuwa ga masu baiyana tsiraici.
ILLAR DINKIN BANZA.
Illolin dake cikin dinkin banza suna da yawa, domin yana daga cikin illar dinkin banza tayar da sha awar mutane.
Wani na iya ganin dinkin dawata tayi yaga wani abu ajikinta sha awar sa ta tashi wanda kuma haka na iya kaishi ga aikata zina, kaga
dinkin banza na yada fasadi a bayan kasa, sannan da yada zinace zinace a tsakanin Al'umma.
kuma aduk lokacin da zinace zinace sukai yawa acikin mutane to rushewar wannan al'ummar ya yi saidai ajira lokaci, zakaga amfada cikin bala'e bala'e, masifu da cututtukan da ba a san kansuba ba sujin magani.
Yawan ganin tsaraici shikansa yana daga cikin abubuwan dasuke rushe tarbiyyar al'umma gaba dayanta.
KADAN DAGA DINKUNAN DA AKE YAYI YANZU.
1. FARALAYS:
Shine wanda za ayi hannu daya yafi daya, daya dogo daya gajere kokuma kasan riga a shanye gefe daya yafi
daya.
2. ZUGE DARLING:
Shine wanda ake masa wata igiya a kirji wanda za a zugeshi zam.
3. FITTED GOWN:
Itace rigar da ake matseta daga kasa har zuwa guiwa ta fitar da siffar wadda tasa ta daga sama har zuwa guiwa idan anzo guiwa sai abude ta.
4. HIGH WAIST:
Itace wacce a ke mata sket dogo sai asa rigar kanti asama mai karamin
hannuu ko babban hannu.
5. JAHANNAMA GA FASINJA.
6. SHOW ME YOUR BACK (NUNA MIN BAYANKI).
7. BREAST CURVE (MAI RIGAR NONO).
8. KEREWA da dai sauransu.
MEYE ZAI HANA DINKIN BANZA?
Abinda zai hana dinkin banza shine jin
tsoron Allah, ganin girmansa da kuma sanin
muhimmancin koyi da karantarwar Manzo
Allah (S.A.W).
Teloli suji tsoron Allah subada suma tasu gudun mawar wajen umarni da kyakykyawan aiki da hani ga mummunan aiki.
mukoma ga addini gaba ki daya bawai addini a masallaci ko makaranta kawai ba, mubar koyi da yahudu da nasara
kan wannan rayuwar duniyar mai ka rewa.
Mu yarda dacewa ba wata wayewa inba wayewar addinin musulunci ba.
Allah yabamu ikon gyarawa.
Wassalamu alaikum wara hamatullah.