•═════❀💠❀═════•
LABARIN MUTUWA TA
•═════❀💠❀═════•
INNALILLAHI WAINNA ILLAIHIRRAJIUUN!!!
A Jiya na dawo gida a gajiye. Sai na gayawa matata cewa zan canza tufafina sannan in d'an kwanta in huta ka'fin ta gama abinci.
Haka naje na canza kayana sannan na kwanta a kan gado na rufe ida'nuna.
Ban bud'e ida'nuwana ba har saida aka kira sallar la'asar.
Sai na tashi na fito daga d'aki na doshi inda matata take dafa abinci
Ina qarasawa gurin sai naga matata sai jera abinci takeyi akan teburi.
Sai na zauna akan tebur
sannan na tambayeta me kika dafamana ne. Rabin zuciyata. Naga tayi shiru.
sannan na qara tambayarta me kika dafamana ne. Rabin zuciyata.
Amma sai tayi shiru ba tace mini komai ba.
Sai na qara tambayarta a karo na 3 da karo na 4
amma sai naga tayi shiru batace komai ba.
Sai raina ya 6a'ci. Amma sai na tina cewa yau shekararmu ashirin muna rayuwa a tare. Amma ban ta6a kiranta taqi amsawa ba.
Sai na waiwaya inda d'ana yake zaune sai nace masa yaje firij ya kawo mini ruwa a kofi.
Amma sai naga shima yayi shiru ya qya'leni. Sai abin ya bani ma'maki. Sai na tashi da niyyar fita daga d'akin girkin.
Kawai sai naji matata ta gayama d'ana cewa yaje d'aki ya taso babansa daga bacci. Sai naji hankalina ya tashi.
Haka d'ana yaje d'akina don ya tasheni daga bacci.
Sai na d'aga muryata nace masa ga'ni anan.
Amma ko waiwayowa baiyiba.
Haka ya doshi d'akina a guje don ya tasoni.
Bayan kamar minti 1 sai ya dawo a firgice.
Sai babarsa ta tambayeshi
shin ka tasoshi ne?
Sai yace: na'yi_na'yi amma yaqi tashi..
Sai matata ta tafi d'akina da sauri d'ana yabita a baya.
Sai na bisu don inga yadda zasu tasoni daga bacci.
Sai naga sunata qoqarin tashin wani mutum mai kama dani da yake kwance akan gadona.
Kuma mutumin ya sanya tufafina.
Da taga ta kasa tashinsa daga bacci, kawai sai hawa'ye ya riqa fitowa daga idonta.
Sai naga ita da y'ay'ana sunata kuka. Sai naga abin kamar a mafarki.
Yaah Ila'hee, wai me yake faruwa ne?
Waye wancan mutumin mai kama dani.?
Me yasa inayi magana basa'ji?
Me yasa basa ganina.
Sai d'ana ya fita da sauri.
Can sai naga ya dawo. shi da babana da babata da wasu y'an uwana, dukkanninsu sunata kuka.
Babata ta riqa rungume wannan mutumin mai kamannina.
Sai naje wajenta na riqa qoqarin ta6ata da yimata magana.
Amma abu ya faskara, sai na juya wajen babana da y'an uwana amma sai naga basa jin muryata.
Sai naji y'an uwana suna maganar ayi mini jana'iza.
Sai mai yin wankan ga'wa yazo ya riqa wanke wannan mutumin mai kama dani da yake kwance a d'aki na.
Y'ay'ana suka taimaka masa aka wanke mutumin aka sanya masa likkafani aka d'aurashi akan makarah.
Abokaina da masoyana suka cika gidanmu suna yima babana da yan uwana gaisuwar makoki.
Sannan suka d'auki makarar suka kaita Masalla'ci.
Kowa ya fita daga gidan mata kawai aka bari.
Sai nayi sauri na fita na nufi masallaci na iske maqwabtana da abokaina sunyi sahu a bayan liman.
Haka na riqa ra'tsa dandazon masu sallah ba tareda na ta6a kowa ba.
Lima'mi yayi Kabbara ta 1.
Ni kuma ina tayi musu ihu, inacewa wai wa kuke salla'ta?
Ga'ninan a atare daku. Ba kwa'gani ne!!!
Magana nake muku ko ba kwa'jina ne?
Alokacin da na fitar da rai cewa zasu kula'ni.
Sai na qya'lesu suka riqa sallarsu.
Ni kuma na nufi inda makara take.
Na cire likkafanin don inga fuskarsa.
Kawai sai naga ya bud'e ida'nunsa
yace mini:
Ni na gama aikina. Kai kuma har abada kaine zaka riqa yin komai da kanka.
Domin adah atare mukeyin komai har tsawon shekaru 40.
Amma yanzu ni qasah zan zama.
Kai kuma hisabi za'a maka.
Ban ankara ba sai jina nayi akan makara, kuma ga66aina sun kaasa motsi. Banda qarfin yin motsi.
Haka suka binneni sukai tafiyarsu.
Tun inajin motsin ta'kalmansu har na daina.
A wannan lokacin ne na fahimci cewa qarshena yazo.
Sai na fara tinanin yadda mutuwa tazo mini bagatatan, alha'lin ayyuka sunyi mini yawa kuma akwai alqawarur_rukan da ban cika ba.
Kuma akwai way'anda suke bina bashi kuma ban rubuta ba.
Ban gayama kowa ba. Banyi wasiya ba.
To yaya zanyi ?
Ga'shi inaso inyi umarni da kyaky_kyawa kuma inyi hani da mummuna.
Ina cikin wannan tinanin ne naji ala'mar ana tafiya an doso inda nake.
Babu makawa Munkaran da Nakiyr ne suka taho inda nake.
Sai na fara ihu ina cewa:
Ya Allah a mayar dani duniya.
A mayar dani duniya.
A mayar dani duniya.
A mayar dani duniya.
Domin in aikata aikin alheri.
Haka nayita fadi' har muryata ta disa'ashe.
Amma aduk lokacin da nace a mayar dani. Sai inji wata murya tana cewa inah. Inah. Ai lokaci yazo qarshe.
Sai naji wata murya a kusa da kunnena ana cemini baba baba baba.
Ina bud'e ido sai naga ashe wata y'atace take ta'shina daga bacci.
Nanfa nayi ajiyar zuciya nayi murmushi.
Na godema Allah s.w.t.
Sai na zauna akan katifa gumi nata fitowa daga jikina zuciya tana bugawa da qarfi.
Nanfa na fara tinanin ayyukan alherin da ya kamata in fara aikatawa.
Don haka y'an uwa kuyi saurin aikata aikin alheri domin rai batasan abinda zai faru a gareta ba gobe, kuma batasan a inda zata mutu ba.
Ya Allah kabamu ikon aikata alkhairi da hanida mummuna.
Via: Rayuwa A Musulinci.
www.tafarkintsira.blogspot.co.ke