INDAI KASAN KANAYIN SEX CHAT TSAYA KA KARANTA WANNAN SAQON.
Daga wani bawan Allah daya nemi mu sakaya sunansa, ga abinda yake cewa kamar haka:
Ni ina daya daga cikin masu aikata wannan laifin daga jiya zuwa yau Allah (S.W.T) cikin ikonso ya shiryar dani a sanadin wadansu illoli da nagano masu yin wannan aiki suna tsintar kansu, ga duk wanda yake aikata wannan mummunan aiki idan nafada yaji zai gasgatani.
Gasu kamar haka:
1. Duk maiyin sex chat shi a karan kansa yasan sabo yakeyi.
2. Idan kanayinsa misali kahau online karfe 9 nadare zakayi estimate nawasu awanni kamar 2 ko 3 kana cikinyi zakaga har sunzo gashi baka samu biyan bukata ba, saika kara wasu kai idan kai wasa sai kakai daya na dare ko 2.
3 wani abin takaici saika gama samun wacce zaku nayi a karshe jayayya tashiga tsakaninku ko rashin yarda, kamar turomin kaza sai tace a'a saika turomin abu kaza, karshe hakan saiya zama sanadin rabuwarku kuna masu jin haushin juna, dama shi aikin sabo haka yake.
4. Idan kana sex chat bakason akawo maka wani uzuri wanda bashiba.
5. Zaka jima kana bata lokaci a online ammafa bazaka gamsuba saidai katayar da sha'awarka karasa wacce zata daukema karshedai saidai kasabi Allah kayi ''ISTIMNA'I''.
6. Lokacin da kake yinsa zaka dinga jin dadi amma idan kashigo cikin jama'a sai kanajin haushin mu'amala dasu.
7. Zaka dinga yawan jin jikinka abushe kuma koda yaushe cikin jin bacci kake da yawan damu, kuma koda cikin mutane kashigo zaka dinga jin kamar baka da gaskiya bakowa kake iya hada ido dashi ba.
8. Zaka dinga yawan mantuwa idan aka gaya maka magana sai an sake maimaitama.
DALILAN DAYASA NADAINA
Mafi yawanci bakama san dawa kake chat ba matar wanice tsohuwace ko yarinya ?
Farace ko baqa kaidai kawai burinka kabiya buqata.
BABBAR ASARAR DANA TAFKA A SANADIN SEX CHAT.
Jiya tun misalin karfe goma da rabi nadare nahau online bani na saukaba sai misalin 4 da minti hamsin gabda za'a tayar da sallar asuba nakama bacci a taqaice sai misalin tara nasafe nafarka.
INNA LILLAHI WA INNA ÏLAIHI RAJI'UN
Wannan itace mafi girman asarar da nayi nake nadamar inama ace kwana nayi ina tasbihi ???
Najima inason tuba amma saina dinga biyewa zuciyata sai jiya Allah yasa nagane ina cutar kaina.
Bazan manta da masu addu'ar rokamin shiriya ba Allah yasaka muku da alkhairinsa dama haka dabi'ar mutanen kirki suke basa la'antar wanda ya kaucewa hanya.
Nayi nadama akan abinda nayi, wadanda sukeyi kuma na rubutane saboda su suji tsoron Allah sudaina, wadanda kuma basayi Allah ya tsaresu.
Ni kuma a karshe dan Allah da annabinsa ku tayani da Addu'ar Allah yasa tubana yazama ''TAUBATAN NASUHA'' dan girman Allah ku tayani da Addu'a 'yan uwana musulmi akan Allah yatsari zuciyata ga komawa wannan kaba'ira da yawanku akwai bayin Allah nagari cikunku Addu'arku tanada muhimmanci gareni, wallahi nayi nadama yanzu haka kuka nakeyi.
Kutayani watsa wannan saqo.
ALLAH YASAKA MUKU DA MAFIFICIN ALKHAIRI.