FALALAR YIN SALATI GA ANNABI (S.A.W).
Abdur-rahman bn Auf (R.A) yace:
Naga Manzon Allah (S.A.W) yayi sujjada, kuma ya tsawaita sujjadar, sannan yadago kansa, sai na tambayeshi gameda haka ???
Sai yace;
"Jibrilu (A.S) ne ya sameni, sai yace dani.
Duk wanda yayi maka salati daya, Allah (S.W.T) zaiyi masa salati, (sau goma).
Wanda yayi maka sallama, Allah (S.W.T) zaiyi masa sallama, (sau goma).
Shine nayi sujjada ga Allah don godiya".
Wannan hadisin Ahmad bn Hanbal ya ruwaito shi acikin MUSNADU hadisi mai lamba 1664.
Sannan Baihaqi ya ruwaito shi hadisi mai lamba 157.
Kuma Hakim ma ya ruwaito shi a juzu'i na daya hadisi mai lamba 550.
Babban abin lura acikin wannan hadisin shine.
Shin me yasa Annabi (S.A.W) yayi sujjada ?
Me yasa yake godiya ?
Amsa itace, yayi sujjada kuma yayi godiya ne saboda wani babban alheri yasamu masoyansa watau mu al'ummarsa.
Wannan yanuna tsananin son da Annabi (S.A.W) yake yi mana, da tsananin bukatar da yake da ita, ta yaga mun sami rahama.
Don haka kada muyi watsi da wannan damar da muka samu.
Mu kara gode ma Allah (S.W.T) daya sanyo mu cikin al'ummar wannan babban masoyi namu, wanda yake murna idan alheri ya samemu.
Kuma mu kara son wannan babban masoyi namu, mahaukacin so, baji ba gani, mu bishi ido rufe kawai, duk abinda ya inganta daga gareshi kada mutsaya wasa, mu kama, mu damka, mu rike, muyi tayi kawai, wannan itace mafita.
Duk wanda bai fahimta ba yanemi karin bayani gun malaminsa.
Sannan daga karshe mukama salatin Annabi muyi tayi, a ko ina muke kuma ko cikin wane hali muke.
Allah ya kara mana son Ma'aikin Allah (s.a.w).
Mutum nawa zasu amsa mini ???