KUNJI BAYIN ALLAH NAGARI!!!
Wata rana wani malami yana sallar dare a gidansa, sai barawo yashiga zaiyi sata barawon ba musulmi bane, sai zuciyarsa taraya masa cewa yashiga dakin malamin.
Yana shiga yasami sabuwar riga ya dauka yagudu malamin yana idar da sallah sai yaga ansace masa riga, sai yafara addu'ah yana mai cewa:
Ya Allah kafini sanin wanda yasace min riga, Allah ka rufa masa asiri.
Yaci gaba dayin addu'ah ya Allah kasa wannan satar tazama alkhairi a gareshi.
¥ Bayan wata (4).
Malam yahada kudi yatafi kasuwa zai sayo riga sai yatarar ana rigama akan rigarsa da barawo yasace masa, ga barawo da riga sannan kuma ga mai saye sannan ga jama'ah sun taru ana rikici.
Malam yace lafiya kuwa ???
Mai saye yace kawai don nace yakawo shaida domin kada insayi rigar sata irin wannan mai kyau a walakantani a gari.
Barawo yagane malamin, shima kuma malam yagane rigarsa.
Sai malam yace ba barawo bane, ni shaidane.
Mai saye dai shikam sai yafasa sayan riga.
Sai malam yabiya kudin riga yadawo gida da kayarsa.
Barawo jikinsa sai yayi sanyi saboda malamin yarufa masa asiri.
Sai yabi malam har gida ya musulunta.
Kunga wannan shine sanadai Arzukin da malam yaroka masa a wajen Allah (s.w.t).
Ya Allah kasamu daga cikin bayinka masu afuwa da kuma yafiya.