Wednesday, 26 July 2017

HIKAYAR LAILA MAJNUN (2)

Tags

♣HIKAYAR LAILA MAJNUN♣

««kashi na 2»»

Zanci gaba daga yadda muka tsaya.

Mun tsaya a inda wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsam yayi ido hudu daLaila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta.

Daga wannan rana Soyayyar Laila tahana Wird yayi bacci a wannan dare !

Cikin yan kwanaki kadan Iyayen Wird suka sauka a gidansu Laila domin neman aurenta ga dansu Wird.

A wannan rana da Iyayen Wird sukaje ga mahaifin Lailasaid a suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar !

Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya.

Bayan hakane Mahaifin Laila yakira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita!

Babbar Magana !

Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai yayi mata barazanar cewar zai yankata idan har bata amince da auren Wird ba !

Kwatsam sai aka wayi gari Qais wato (majnun) yaji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure, da Wird.

Wanne irin hali Qais zai kasance a wannan ranar ?

Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din!

Waqe-waqen soyayya sune zancensa, bashida abokin hira sai wakar dayake yiwa laila.

Ga kadan daga irin abinda yake cewa:

Zuwa ga Allah nake kai kukan son laila kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa ga Allah.

Marayan da da kafarsa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshi Lallai rasa iyaye abune mai girman gaske.

Haka Qais da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah” yake bin kwararo-kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gusheba har saida akayi masa lakabi da “majnun" wato mahaukaci.

Tun daga wannan lokaci wannan suna yake binsa.

Muhadu a darasi name 3