☀TAMBAYOYIN TAFARKIN TSIRA☀
««fatawa ta 63 »»
Assalamu Alaikum.
Malam ban wuce shekaru goma sha daya ba a duniya, amma na shiga bandaki sai naga wani jini yafito min, har yafara jika karamin wandona (pant), to malam shin wannan jinin haila ne ko kuma na cutane ?
Don naga kamar shekaruna basu kai nayi jinin haila ba.
Allah yayi makaalbarka a rayuwa.
(Daga Fatima Abbas).
AMSA:
-----
Ameen
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 ko 09-60 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50 wannan ya danganta da irin yanayinta da kuma wurin da take zaune.
Malamai sunyi sabani shin akwai wata shekara ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin daya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za’a kira shi jinin haila ba ???
AMSA
-----
Darimi -Allah yayi masa rahama- yace bayan ya ambaci sabanin da akayi:
(Wannan duk kuskure ne awajena).
Domin abin lura shine samuwar jinin, don haka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekarane ya wajaba a sanya shi yazama haila”.
Wannan abin da Darimi yafada shine daidai saboda Allah da manzonsa sun rataya hukunce- hukuncen jinin hailane da samuwarsa, basu kuma iyakance wasu shekaru na musamman ba, kamar yadda Ayah ta: 222 a Suratul Bakara take nuni.
Wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili na daga litttafin Allah ko daga sunnar Manzonsa, ba’a kuma samu ba.
Saboda haka jinin da kika gani sunansa jinin haila, kamar yadda malamai suka fada duk jinin daya fito daga gaban mace sunansa jinin haila mutukar ba’a samu wani dalili da yake nuna cewa na cuta neba.
Allah Shine mafi sani.
Don neman karin bayani kuduba:
(Dima’uddabi’iyya, shafi na: 6).