Tuesday, 2 January 2018

YADDA AKE YIN WANKAN JANABAH

Tags

YADDA AKE YIN WANKAN JANABAH.
==============

Salam, malam dan Allah kayi mana karin bayani akan wankan janaba da wankan haila dan har yanzu akwai masu damuwa akai.

(daga Abdullahi mani babba)

AMSA
====
Da farko Idan Mutum yashiga Bandaki (bathroom) Zai farane da wanke Najasar dake tare dashi.

Ma'ana, Zai Fara wanke Al'aurarsa, da kuma duk wuraren da Maniyyi (ko jinin) ya taba ajikinsa.

(Misali tun daga Cibiyarsa har zuwa cinyoyinsa).

* Kuma Zai Qulla niyyah ne yayin da yake wanke Al'aurarsa.

* Sannan saiya wanke dukkanin Gabobinsa na Alwala.

Amma sau dai-dai ko 2 ko 3 duk wanda mutum yayi daidaine.

* Idan kaga dama zaka bar Qafafunka, Sai akarshen wankan.

* Sannan Saika wanke Kanka Sau Uku.

(tare da wuyanka da fuskarka gaba dayanta).

* Saika wanke tsagin Jikinka na Dama, har zuwa Kafarka ta dama.

* Sai kuma tsaginka na Haggu, kahada har Qafarkata haggu din.

* Ya zama wajibi kacire zobe daga hannayenka (Idan ya matseka) kuma dole ka Tsetsefe dukkan yatsunka na hannu dana Qafa.

* Ka chuda Kafarka sosai.

Musamman idan inhar kanada kaushi.

* idan kazo wanke kowanne tsagi, ka tabbatar da cewa kana Chutchuda Bayanka sosai.

* Idan kuma hannunka baya iya kaiwa, sai kasamo wani Tsumma ko Kyalle mai tsafta, KaJiqa-shi, Sannan ka Chutchuda dashi.

* dole ne ka chutchuda Ko ina ajikinka.

Musamman ma idan kana da Qiba.

* Dolene Ka wanke Duburarka sosai tun farko.

Kada kayi la'akari da cewar "Ai bakayi bahaya ba".

A'a. Ai nan dinma jikinka ne.

Idan baka wanke taba, to wankanka bai yiwu ba.

* Ka kula da Ramin cibiyarka.

Ka tabbatar cewa Ruwa yashiga har nan.

* Ya zama dole 'yan uwa mata su tabbatar cewa Ruwan ya ratsa har cikin Kitsonsu yayin wankan.

* Namiji idan yanada gemu, to lallai ne ka tabbatar cewa ka Tsetsefe shi komai Kaurinsa da duhunsa.

~~ ~~ ~~ ~~ ~~ ~~ ~
NOTE: Zaka iya amfani da wannan alwalar kayi sallah, wacce kayi yayin wankanka.

Indai har baka sake ta'ba al'aurarka ba bayan kayi alwalar.

HAKA AKE YIN WANKAN JANABA, HAILA, NIFASI, DA KUMA WANKAN SHIGA MUSULUNCI.

Wallahu A'alam.