KANASO A AMSA ADDU'ARKA ???
Annabi (saw) yace:
Mutun uku idan sukayi addua ba'a dawo ita ana amsata alokacin sune:
1. Wanda aka zalunta yanemi agaji awajen Allah.
2.wanda yake yawan zikiri (ambaton Allah)
3. Shugaba adali mai adalci ga jamaarsa.
Tambihi:
Dayawa muna daukar cewa kalmar shugabanci ta rataye akan masu riqe da muqaman siyasa.
To a gaskiya abin ba haka yake ba.
A matsayinka na magidanci kaima shugabane, amatsayinki na matar gida kema shugaba ce.
Awani hadith manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
كلكم راع وكلكم مسؤل أن رعيته
"DUKKANIN KU MASU KIWO NE KUMA DUKKANINKU SAI AN TAMBAYEKU AKAN ABIN DA AKA BAKU KIWO"
Allah ya gafarta mana zunubanmu baki daya.