Tuesday, 2 January 2018

ABUBUWAN DAKE KAWO WARIN GABAN MACE DA HANYOYIN MAGANCESU.

Tags

ABUBUWAN DAKE KAWO WARIN GABAN MACE DA HANYOYIN MAGANCESU.

Assalamu Alaikum

Malam menene yake sawa gaban mace yana wari kuma menene maganinsa.

(Daga Zainab Adam)

AMSA
-----
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

Ga Kada cikin Abubuwan dakesa gaban mace yana wari.

1. Tafiya babu wando.

2. Rashin sanya takalmi, koda kuwa acikin gidane.

3. Dadewa akan masai (toilet).

4. Rashin canza pant da wuri.

5. Yawaita cin danyar albasa.

6. Istimna'i wanda ake kira Masturbation a turance (wato mace ta biyawa kanta buqata ta hanyar wasa da gabanta.

7. Tsarki da ruwan sanyi.

8. Rashin aske gaba, dadai sauransu.

YADDA ZA'A MAGANCE WANNAN MATSALA DA YARDAR ALLAH.

1. Mace ta dinga tsarki da ruwan dumi.

2. Kidinga yawan canza wando a kullum kamar sau 2 ko 3.

3. Ki rage cin danyar Albasa.

4. Aduk lokacin da mace tagama haila ta dinga wanke gabanta da ganyen magarya koda farin almiski.

5. Sannan ta daina tsugunawa akan masai tana daukar tsawon lokaci.

6. Ta yawaita aske gabanta duk sati 1 ko 2.

Wadannan sune kadan daga cikin shawarwarin dazan bayar da fatan mata zaku kiyaye.

Kada wadansu suga kamar nayi batsa harkar addini saida tsafta.