TAMBAYOYIN TAFARKIN TSIRA
««fatawa ta 104»»
Salam Malam Ya kamata ace nayi istibra’i kafin nayi aure, amma banyiba, har nayi aure, yanzu haka ina jini na farko banyi tsarki ba, amma bada wanda na aikata laifin cikin nayi aure ba.
Yaya ingancin aure na?
Gani nake kamar babu auren ko ?
(Dan Allah ka6oye sunana)
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Da farko dai inayi miki wasici da tsoron Allah, saboda zunubin da kika aikata na zina, amma gameda aure, shi aurenki yayi, saidai yinsa bayan istibra’i shine yafi alkhairy, sannan ya wajaba mutukar kinsan kinada ciki to bai halatta kibawa sabon mijinki dama ya take kiba ma'ana ya sadu dake.
Saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi:
“Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa”.
(Abu-Dawud: hadisi mai lamba 1847).
Don haka, ya wajabta a gareki kiyi stibra’i kafin mijinki yasadu dake, sannan istibra’i jini dayane, idan kuma har kin dauki ciki, kafin kiyi istibra’i, in kin haihu kafin wata shida to ba ‘dansa bane, amma in har kin haihu bayan wata shida (6) daga fara saduwarku, to ‘dansa ne, mutukar ba’a samu shaidar da take nuna kinada ciki ba, tun kafinku fara saduwar.
WALLAHU A'ALAM
DominIn neman Karin bayani kuduba: (Al-mugny na Ibnu Qudaamah, mujallady na 8\79).
Tuesday, 2 January 2018
Ya kamata ace nayi istibra’i kafin nayi aure, amma banyiba,
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)