Tuesday, 2 January 2018

INA SAMARI DA 'YAN MATA MARASA AURE KADA KUWUCE WANNAN SAQO BATARE DA KUN KARANTA BA.

Tags

INA SAMARI DA 'YAN MATA MARASA AURE KADA KUWUCE WANNAN SAQO BATARE DA KUN KARANTA BA.

ISTIMNA'I a "Larabce"

Ko kuma (Mastubartion) a turance:

Shine Biyawa kai bukata wani bala'ine dayake addabarmu, a gefe guda shima mutane dayawa basu daukeshi a matsayin laifi ba amman laifine babba saboda Allah yana fushi da me yinsa.

Sannan kuma yana haifar da illoli da dama.

Mata da maza nayinsa.

Mace tana amfani da hannunta wajen sanyawa a farjinta don biyawa kanta bukata, ko tasa wani abu ko kuma kallace kallacen banza na (Blue Film).

Haka suma maza suna yinsane ta hanyar wasa da alkalaminsu mazaqutarsu ko makamancin haka.

Illolinsa kuwa sune:D

Duk sperm maniyyin daya fita ba a bisa ka'ida ba to baya fita gaba daya.

Wannan ragowar yana haifar da matsaloli da yawa kamar haka:

Ga mace yana sanya mata cancer mahaifa sannan ga matsanancin infection da warin farji.

Maza kuma yana Qankantar da alkalaminsu sannan yana haifar da daqushewar kwakwalwa, sannan yanasa karkarwar jiki da yawan mantuwa a Qarshe masana sunce yanasa Qaramin hauka.

Sannan yana sanya yawan kasala masu yinsa daga mace har namiji basa yawan zama cikin mutane, zakaga suna yawan kebewa shiru su kadai.

Dan haka kalubale gareku iyaye kusa ido akan 'ya'yanku idan kun gansu shiru acikin daki ku fiddosu waje cikin dabara kuma yanzu ba yayin kunya bane a addini kina iyayiwa 'yarki nasiha da wa'azi harda tsoratarwa sannan idan kikaga yarki maison aurece dan Allah kada kibi son zuciya kiyi mata ki rakata da addu'a saboda gudun fadawa cikin bala'in da a gobe kiyama Allah zai tuhume ki.

Hanyoyin barinsa yana da sauki.

Anaso mutum ya lazumci azumi koda alhamis ne da litinin, sannan a daina zama shiru a daki.

A dage da addu'a.

Dan Allah kuyi like da share saboda 'yan uwanku su amfana.

Muna fatan Allah ya yaye mana, kuma yakara mana tsoronsa.