Tuesday, 2 January 2018

HUKUNCIN ZAGIN NANA A'ISHA UWAR MUMINAI (R.A).

Tags

HUKUNCIN ZAGIN NANA A'ISHA UWAR MUMINAI (R.A).

Kana iya cewa Ijma'ine Malamai suka yi akan duk wanda yazagi Uwar Muminai, ya kuma dangantata ga abinda Allah ya tseratar da ita daga gareshi, mai yin haka ya Kafirta kowane ne.

1- Al-Qadi Abu Ya'ala yana cewa:

(Duk wanda yayima A'isha Qazafi da abinda Allah ya tseratar da ita daga gareshi to ya kafirta babu ko tantama).

2- Imamu Darul Hijra (Malik bn Anas) Allah yayi masa Rahama yace:

Duk wanda ya zagi Abubakar to ayi masa bulala, ko wanda ya zagi A'isha to a kashe shi.

Sai akace:

Saboda me?

sai yace:

Wanda ya zageta haqiqa ya sa6a kuma yayi fito na fito da Al-Qur'ani.

[Domin Qarin Bayani kuduba Assarimul Maslul shafi na 565 zuwa shafi na 566]

3-Ibn Sha'aban ya rawaito daga Imamu Malik yana cewa:

Saboda Allah ta'ala ya wanke Nana A'isha daga yarfe da 'kagen da akayi mata:

(Allah yana gargad'inku kada ku sake yin kwatan-kwacin wannan, matu'kar dai ku Muminai ne).

[Suratun Nuur aya ta 17]

Saboda haka sai yace to duk wanda ko ya 'kara zaginta ko jingina mata wannan 'kazafi to haqiqa ya Kafirta.

4-Imam Ibn Kathir yace:

(Ha'ki'ka Malamai sunyi Ijma'i akan cewa lallai duk wanda ya zageta da irin kwatankwacin abinda wannan ayar ta wanketa dashi, bayan saukar ayar to ya kafirta domin yana fad'ane da Al-Qur'ani).

[Tafsirin Ibn Kathir mujallady na 3/276 a Qar'kashin Tafsirin "Innal-ladhina yarmunal Muhsanat...." Suratun Nur 23.

5- Sannan Mai tarin sanin nan acikin Ilimin Hadisi wato Ibn Hazam (Azzahiry) yana mai yin Ta'aliqin Maganar Imam Malik (Ra) yace:

(Maganar Malik anan dai-daice, yace bugu da Qari yin hakkan Riddace cikakkiya kuma 'karyata Allah me girma da daukaka acikin yankewarsa da yayi na tseratar da ita.)

Intaha.

Mai neman Qarin bayani ya iya duba Littafin Al Muhalla na Ibn Hazam 11/415.

Saboda haka duk wanda yazagi daya daga cikin matan Annabi (S.A.W) kamar yafita daga Muslunci ne.

Allah ka kiyaye mu.