Wata rana wani Shehin malami yana zaune a ofis sai wata daliba tashigo tayi sallama
tace masa:
"Malam nazo duba sakamakon jarabawata, amma dalibai sun yage takardun.
Dan Allah ka taimakamin karoki Exam officer a nuna mun tawa.
Sai Malamin yatashi yashiga ofishin Exam officer yace idan babu damuwa kuma ba a sa6a doka ba, a taimaka a nuna ma wannan dalibar sakamakon jarrabawarta.
Sai suka ce ai Malam tunda ta biyo ta wurinka duk da baka san ta ba, za'a bata ta duba da kanta.
Bayan an baiwa wannan daliba tana dubawa, zuwa kan sunanta keda wuya sai kawai sukaga tarufe takardan da sauri tafashe da kuka ta juya ta fita.
Fitar wannan 'daliba keda wuya, sai Malaman nan suka ga Shehin Malamin nan yana zubda kwalla, har takai ga yakasa mallakar idanuwansa.
Bayan an nutsu ka'dan, Sai Malaman suka cewa Shehin malamin nan, Akramakallahu muma kasa zukatanmu sun tsinke, saboda ita wannan yarinya ko bamu tambaye taba munsan sakamakon
jarabawace da bata yi mata kyau ba.
Amma kai kuma sai muka rasa dalili, amma munsan dukkan abin da zai sanya ka zubda kwalla lallai wannan abun ba karami ba ne.
Sai Shehin malamin nan yace musu:
"Wallahi lokacin danaga wannan yarinyar tafashe da kuka sai zuciyata take cemin
YANZU INDA SAKAMAKON LAHIRA NE MUTUM YA TARAR DASHI A HAKA YA ZATA KAYA ?"
Yace wannan shine abin daya tsorata ni saboda anan ana iya gyara, amma banda Lahira.
Saboda haka, mu ma 'yan uwa saimu hankalta,
MUTUNA CEWA AKWAI DUBA SAKAMAKO A
RANAR LAHIRA!!!
Muna rokon Allah yasa muga sakamako mai kyau a ranar lahira.
Tuesday, 2 January 2018
MUTUNA CEWA AKWAI DUBA SAKAMAKO A RANAR LAHIRA!!!
Tags
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)