Wednesday, 13 December 2017

GA WANI WA'AZI AKAN ZAMAN DUNIYA MAI DAUKE DA TARIN DARASI.

Tags

GA WANI WA'AZI AKAN ZAMAN DUNIYA MAI DAUKE DA TARIN DARASI.

Duniya duk jaruntar mutum, wata rana saita mayar dashi rago.

Duk iliminka wata rana saita mayar dakai kamar jahili.

Duk isarka, wata rana saita mayar da kai Qasqantacce.

Abinda yake baka tsoro ada, wata rana sai yabaka tausayi.

Abinda yake baka haushi, wata rana sai yabaka dariya.

Idan kana ganin kafi kowa, wata rana zakaga wanda yafika.

Idan kana ganin kowa yafika, wata rana zaka ga wanda yafika talauci.

Wanda yake zaginka, wata rana zai wayi gari babu abinda zai zaga.

Wanda ka tsana, wata rana zaka wayi gari ya mutu balle kaji haushinsa.

Wanda kake Qi, wata rana shi zakaso.

Wanda kuma kakeso wata rana shi zaka Qi.

Idan ka zalunci wani don kafi karfinsa, wata rana wani zai zalunceka don yafi karfinka.

Idan katuno wani abu, sai yasa kayi kuka mai yawa, wata rana kuma idan ka tuno wani abu, sai yasa kayi dariya mai yawa.

'Yan'uwa kawai dai muyi fatan Allah yasa muci jarabawa, domin duniyar nan ta wuce tunanin mu.
Hakika duniya itace gonar lahira.

Allah kabamu ikon shuka alkhairi kuma mu girbi alkhairi mai tarin yawa.