RAYUWA BAYAN MUTUWA (1).
Dayawa daga cikin mutane suna zaton idan sun mutu aka binne su shikenan rayuwa taqare daga nan.
Wannan fahimta an ginata akan kuskure babba kuma mummuna.
Mutum bayan ya mutu yana shiga wata sabuwar rayuwa.
Akwai rayuwa ta zaman qabari, da rayuwa ta bayan hisabi.
Zan dan yi tsokaci acikin littafin Allah da Hadisai ingantattu a kan wannan al’amari.
Tareda fito da al’amarin a fili na abin dazai kasance bayan mutuwar.
Idan mutum yamutu, anbinne shi, farkon rayuwar dazai fara fuskanta shine fitinar qabari.
Hadisi ya tabbata acikin Bukhari da Muslim daga Anas dan Malik.
Manzon Allah (S.A.W) yace:
“Idan bawa yamutu aka sashi a cikin qabarinsa yana jin motsin takalman wadanda suka kawo shi.
Sai mala’iku biyu suzo masa.
Saisu zaunar dashi, suce masa:
"Meza kace dangane da wannan mutum?
To mumini sai yace:
"Na shaida haqiqa shi bawan Allah ne, kuma manzonsa ne.
Sai ace dashi kalli mazauninka na wuta, amma yanzu Allah ya sauya makashi da gida a aljannah.
Sannan duk zai gansu a lokaci daya.
Qatada yace:
Manzon Allah yace:
"Za'a bude masa qabarinsa tsawon zira’i saba’in.
Za ace da kafiri, ko munafiqi:
"Me zakace dangane da wannan mutum?"
Sai yace:
"Kawai nima ina fadar abin da naji mutane suna fada.
Za ace masa.
"Ba ka sani ba, kuma baka karanta ba ?
Sai a doke shi da wata guduma ta qarfe, zaiyi wata qara mai qarfi duk wanda yake wajen zaiji ta, in banda mutum da aljan.
Allah ka tsaremu daga dukkan nau'i na azabarka, ka lullubemu da rahamarka.
Wednesday, 8 November 2017
RAYUWA BAYAN MUTUWA
Penulis tafarkintsira
Diterbitkan November 08, 2017
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)