Wednesday, 26 July 2017

HIKAYAR LAILA MAJNUN (1)

Tags

♠HIKAYAR LAILA MAJNUN♠

««kashi na farko»»

Wane majnun?

Wani mutumne da akayi a daular banu umaiyya abisa zance mafi inganci.

Sunansa na asali shine Qais Bn Mulawwah daga Qabilar Banu Amir.

Qais balaraben kauyene, ya taso tareda ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BINT MAHDI IBN SA’D.

Amfi saninLaila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balaga.

A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais yarude soyayyarsa gareta, hankalinsa ya dugunzuma yatashi.

Domin a wannan lokacin ne Qais ya Llura da irin kyawun dirin da Allah yayiwa abokiyarsaLaila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi takeyi a cikin zuciyar Qais.

Ana cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila yanemi da Qais yafito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna saida Qais ya bayar da raquma guda hamsin gidan su Lailaa matsayin kudin aure.

Ana haka sai ga wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsam yayi ido hudu daLaila a wata rana acikin wani Lambu tana kiwon dabobinta.

Daga wannan rana Soyayyar Laila tahana Wird yayi bacci a wannan dare!

Cikin yan kwanaki kadan Iyayenm Wird suka sauka a gidan suLaila domin neman aurenta ga dansu Wird.

A wannan rana da Iyayan Wird sukaje ga mahaifin Laila said a suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais majnun yabayar !

Muhadu a darasi name 2