Wednesday, 8 November 2017

MIJINA YANAYIN KWAI.

Tags

MIJINA YANAYIN KWAI.

Ko akwai darasi acikin wannan labarin ?

Muhd Sabiu Yakub wrote:

Wata rana wani mutum ya auri sabuwar amaryarsa, suna cikin fira sai dadin fira ya kamashi.

Sai yace da wannan amaryar tasa.

Nagaya miki wani sirri nawa bazaki gayawa kowaba ?

Sai amarya tace Eh angona.

Sai yace da ita:

Nifa inayin kwai kamar yadda kaza takeyi.

Sai amarya ta gyara zama tace da gaske kake ?

Sai yace Eh amma dan Allah kada ki gayawa kowa.

Sai tace to.

Wata rana wata qawarta tazo wajenta suna cikin fira sai tace da ita:

Zan gaya miki wani sirri amma dan Allah kada ki gayawa kowa.

Sai tace to.

Sai amarya tace mata mijina yanayin kwai.

Sai tace mata ke banason karya sai tace:

Wallahi shine ya gaya mini yace kada na gayawa kowa.

Sai tace to shikenan kada kisami damuwa.

A karshe dai wannan kawa ta gayawa kawarta har zance yaje kunnen sarkin garin.

Sai yasa aka kirawo wannan mutumin yace masa:

Wane Labari nakeji acikin gari cewa kanayin kwai menene gaskiyar wannan maganar ???

Sai kunya takama mutuminnan yarasa abinda zaice.

Daga can yadago kai yakalli sarki yabashi amsa da cewa:

Ranka yadade Matata nakeso na jarraba shiyasa na tsokaneta da haka:

Gaskiya amana tayi karanci a wannan zamani.

Allah kabamu ikon kame bakinmu.