♣HIKAYAR LAILA MAJNUN♣
««kashi na 4»»
Mun tsaya a inda Qais wato majnun yake cewa:
Ya Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba.
A taqaice haka majnun yarayu cikin wannan yanayi na abin tausayi!
Ita kuwa Laila tuni WIRD wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi.
Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni saida rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya !
Daga nan itama takamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar da take yiwa Qais Majnun!
Tana cikin wannan haline na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta!
A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta saida yaje har kasar Iraqi yanemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta yatare da zama.....!
Koda yaushe bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta.
Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais- wato Majnun) yakifa cikinsa akan qabarinta, koda akazo aka duba sai aka tarar Allah yayi masa cikawa!
Allahu akbar
Wannan shine Qarshen hikayar "LAILA MAJNUN" kunjifa yadda akeyin soyayya ruwa-ruwan ta.
Hakafa Allah yake jarabtar wasu da soyayya.
Ya Allah kada ka jarabcemu da soyayyar da bazamu iyaba.
Wednesday, 26 July 2017
HIKAYAR LAILA MAJNUN (4)
Penulis tafarkintsira
Diterbitkan July 26, 2017
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)