Wednesday, 26 July 2017

GA WADANSU MANYAN LAIFUFFUKA GUDA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKINSU ???

Tags

GA WADANSU MANYAN LAIFUFFUKA GUDA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKINSU ???

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan
laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda za'a guje musu.

Gasu kamar haka:

1- Shirka da kashe-kashenta.

2- kisan kai.

3 - Tsafi.

4- Wasa da sallah.

5- Hana zakka.

6- Sabawa iyaye

7- Cin riba.

8- Cin dukiyar marayu.

9- yiwa Annabi saw karya.

10- Karya Azumi da gangan.

11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.

12- Yin Zina.

13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.

14- Shan giya da sarrafata.

15- Girman kai da takama da jiji da kai.

16- Shedar Zur.

17- Luwadi da mdigo.

18- Yin kage ga muminai.

19- Satar dukiya daga baitul mali.

20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.

21- Sata, da sane.

22- Fashi da makami.

23- Rantsuwa akan karya.

24- Yawan karya.

25- Wanda ya kashe kansa da gangan.

26- Mugun Alkali,

27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi da maza.

28- Masu auran kisan wuta.

29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir.

30- Rashin tsarki daga fitsari.

31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili.

32- Munafinci

33- Ha'inci

34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani.

35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi.

36- Karyata kaddara.

37- magulmaci.

38- Mai yawan la'antar mutane tsinuwa.

39- mayaudari.

40- Gasgata bokaye da yan tsibbu.

41- Mace mai tsiwa ga mijinta.

42- Rashin sada zumunta.

43- Sassaka gumaka.

44- Annamimanci.

45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi).

46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.

47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.

48- Kafurta mutane, babu dalilin daga sharia.

49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.

50- Zagin bayin Allah malamai.

51- Jan tufafi a kasa,

52- Sanya tufafin alhariri,

53- Yanka dabba da sunan wani wanda ba Allah ba.

54- Wanda ya shiga iyakar kasar wani, ko gonar sa ko filinsa.

55- Zagin sahabbai.

56- Mace mai karin gashi da zane, da yin wushirya da aske gashin gira.

57- Kiran Mutane zuwa ga bata, ko koyar da barna.

58- Wanda yake yiwa dan uwansa barazana da makami.

59- Mai daukan rahoton musulmi yana kaiwa makiyansu.

60- Tauye mudu.

61- Jayyaya da musu mara amfani a cikin addini.

62- Mutumin da baya jingina kansa ga iyayansa.

63- fidda tsammani daga Rahmar Allah.

64- Camfi.

65 - Shan ruwa ko abinci a kofin zinare.

66- Gaba da juna.

67- Butulci.

68, Caca.

69- Keta alfarmar haramin Macca da Madina.

70 - Cin Zarfin makoci.

YA ALLAH KA TSAREMU KA TSARE MANA IMANINMU.