Wednesday, 26 July 2017

HIKAYAR LAILA MAJNUN (3)

Tags

♣HIKAYAR LAILA MAJNUN♣

««kashi na 3»»

Mun tsaya a inda Qais wanda ake yiwa lakabi da “Majnun lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawaLaila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gusheba har saida akayi masa lakabi da “majnun wato (mahaukaci) !

Zanci gaba.

Duk dacewa itama Laila tana matukar son Qais wato (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, bayan yin amfani da mallakeshi datayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun acikin wani baiti nasa yace:

“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane ?”

Sai Malamin ya fadawa Qais cewa:

“Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I.

Daganan Qai yace, saina kasa mallakar idona saida hawaye ya zubo cikin sauri yajiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah yayafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne saboda son da nakeyi mata.

Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har saida yasami tabin hankali wato hauka.

Domin ya kasance idan yaga yara sunayin wasan kasa yakan zauna tare dasu yataro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara sukeyi da kasa yana cewa cikin waqa:

Abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!

A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka baiwa mahaifin Majnun wato Qais shawara daya daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarceshi daya roqi Allah ya cire masa son Laila!

Amma saboda tsananin soyayya a yayin da sukaje dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa:

kama tufafin ka’aba karoki Allah ya cire maka son Laila.

Sai Majnun yakama yace:

“Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Lailaba...

A taqaice haka majnun yarayu cikin wannan yanayi na abin tausayi !

Muhadu a darasi name 4