Wednesday, 26 July 2017

DAGA HALAYYAR MAGABATA 1

Tags

Wata rana wani mutum yazo wurin Manzon Allah (S.A.W) sai yace:

Ya Rasulullah zan tambaye ka gameda rayuwar Duniya data lahira.

Sai manzon Allah ya yadda ya tambaya zai Amsa masa.

Ga tamboyoyin da amsoshin kamar haka:

1. Tambaya :

Ya manzon Allah, Ina son in zama mafi sani acikin mutane.

Amsa : kaji tsoron Allah kabi dokokinsa, zaka zama mafi sani a cikin mutane.

2. Tamabaya : Ina son in zama mafi arziki acikin mutane.

Amsa : ka zama mai wadatar zuci, zaka zama mafi arziki a cikin mutane.

3. Tambaya : Ina so in zama wanda yafi kowa a cikin mutane.

Amsa : wane yafi kowa acikin mutane shine mafi alkhairin su, kazama mai amfanar wa ga mutane.

4. Tambaya : Menene zai kare ni daga shiga wuta ???

Amsa : Azumi

5. Tambaya : Ina son in zama mafi adalci a cikin mutane.

Amsa: ka sowa 'yan uwanka abinda kake sowa kanka zaka zama mafi Adalci a cikin mutane.

6. Tambaya : Ina son in zama mafi amfani mutane a wajen Allah.

Amsa : Ka yawaita tuna Allah, zaka zama mafi amfanin mutane a wurin Allah.

7. Tambaya : Ina so in zama wanda yafi kowa Sadaukar da rayuwarsa ga Allah.

Amsa : Ka bautawa Allah kamar kana ganinsa idan kai baka ganinsa to shi yana ganin ka.

8. Tambaya : Ina son Imani na yazama Ingantacce.

Amsa : Ka gyara halayenka, Imaninka zai Inganta.

9. Tambaya : Menene yake huce fushin Allah.

Amsa : Bada zakka a boye dakyautawa Yan'uwa.

10. Tambaya : wane zunubi ne mafi muni a wurin Allah.

Amsa : Mummunan Hali shine rowa.

11. Tamabaya : Ina son in zama mafi biyayya ga Allah.

Amsa : kabi umarnin Allah zaka zama mai biyayya ga Allah.

Allah yasa mu dace ameen.

Ya Allah ka karbi Ibadanmu baki daya.

Dafatan zamuyi koyi da wadannan halaye nagari.