Friday, 16 June 2017

menene hukuncin mai zuwa gidan abokinsa yana fira da matarsa alhalin abokin nasa bayanan ???

Tags

Assalamu Alaikum

Malan menene hukuncin mai zuwa gidan abokinsa yana fira da matarsa alhalin abokin nasa bayanan ???

(Daga Abdullahi Baban Saifalah).

AMSA
====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

A'a wannan bai halatta ba, yin hakan kusancine ga aikata zina.

Saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) wanda yake cewa:

"LAA YAKLUWANNA AHDUKUM BI IMRA'ATIN ILLA MA'A ZY MAHRUMIN"

Fassara

"Kada dayanku ya kadita da wata mace sai tareda zu maharruminta.

Ma'ana

Dan uwanta wanda babu aure a tsakaninsu, kamar wanda suke uwa daya ko uba daya ko kuma uwa daya uba daya ko makamancin haka.

A Wani hadisin kuma yana cewa:

"لا يخلون رجل بامرأة الآكان ثالثهماالشيطان"

Abinda hadisin yake koyar damu shine:

"Duk wanda ya kadaita ma'ana ya ke6anta da wata mace wacce ba muharramar saba, to zai kasance na ukunsu shaidanne.

To kaga kuwa wata rana idan sha'awarta ta motsa komai zai iya faruwa kasancewar babu mai dauke mata sha'awar tata a kusa.

Saboda haka bai halattaba, aikata hakan zunubine mafi girma.

WALLAHU A'ALAM