Friday, 16 June 2017

MALAM NASHA NONON MATATA MENENE MATSAYIN AUREN MU ???

Tags

MALAM NASHA NONON MATATA MENENE MATSAYIN AUREN MU ???

Don Allah malam ya matsayin mutumin da yasha nonon matarsa, ya aurensu yake ?

(Daga Hamza Sa'eed).

AMSA:
======
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in banda dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila.

Saboda haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa aciki, amma idan akwai ruwa aciki, to malamai sunyi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu kamar haka:

1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shine wanda aka sha kafin yaro yacika shakaru biyu, saboda fadin Annabi (S.A.W).

“Shayarwar da take haramtawa, itace wacce yaro yasha saboda yunwa”

Kuduba Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta :5102.

Ma’ana.

Lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shine abincinsa, shi kuma wannan ya farune bayan mutum ya girma don haka ba zaiyi tasiri ba wajen haramta aure.

Wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

2. Bai halatta ya shaba, saboda koda yaushe mutum yasha nonon mace tota haramta a gareshi, domin Annabi (S.A.W) ya umarci matar Abu-huzaifa data shayar da Salim, don ta haramta a gareshi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2636, tare da cewa a lokacin Salim yariga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba yasha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure.

Zancen da ya fi karfi shine ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shine yafi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau, don neman Karin bayani kuduba:

Bidayatul-mujtahid mujallady na 2\67.

Allah shine mafi sani.