Friday, 16 June 2017

Qissar wani mahaukaci mai suna BAHLU

Tags

Qissar wani mahaukaci mai suna BAHLU wanda yarayu a zamanin sarki HARUNA Ar-RASHEED (Abu Ja'afar Bnul Mansoor Al-Khaleefatul Abbasiy).

Wata rana Bahlul yana zaune abisa kabari, saiga Sarki Harun Rasheed, zai wuce a bisa doki tare da masu bashi tsaro, sai sarki Harun ya kalli Bahlul yace masa:

"Yaa kai Bahlul yaa kai wannan mahaukaci wai yaushe zakayi hankali ???

Sai Bahlul ya sauka daga kan kabarin, yahau can kan wata doguwar bishiya, sannan yadaga muryarsa sosai yana cewa:

"Yaa kai Harun yaa kai wannan mahaukaci yaushe zakayi hankali ???

Tirqashi in banda mahaukacin da anriga an san cewar mahaukaci ne, wanene a zamanin ya isa yadubi Sarki Abu Ja'afar yace masa mahaukaci ???

Sai sarki Haruna ya zaburi dokinsa yakara kusantar bishiyar da Bahlul yake akai, yadaga kansa mai dauke da ado na sarauta, ya kalli Bahlul a sama a zaune yace masa:

"Yanzu nine mahaukaci lo kuma kai da kake zaunawa a kan kabari ???

"TIRQASHI"

Sai Bahlul yace:

"ina ai ni inada hankali"

Sai Haruna Ar-rasheed yace masa:

"Tayaya kuwa haka zata kasance ???"

Sai Bahlul yanuna yatsansa zuwa ga gine- ginen benayen fadar Harun Ar-rasheed.

Yasake bashi amsa da cewa:

"saboda ni nasan wadancan masu karewa ne"

Ya cigaba da cewa:

"Wannan kabarin kuwa shine tabbas, shi yasa na rayashi, kuma nadawo natare a wajensa, kai kuwa sai ka ruguza naka kabarin kagina benaye a duniya, shi yasa baka son zuwa inda naka yake, kariga ka rusa shi!!!"

Bahlul ya karasa maganarsa da cewa:

"To kafadi mini wanene mahaukacin tsakanin ni da kai?".

Harun yayi kuka har saida gemunsa yajike da lema, sa'ar nan yace:

"Wallahi kafadi gaskiya".

Sai yace:

"kara mini wani wa'azin yaa Bahlul".

Sai yace masa:

"Littafin Allah Al-Qur'ani ya isheka wa'azi".

Harun yana jin ya fadi haka sai yace:

"To kana da wata bukata in biya maka ita ?"

Sai Bahlul yace:

"kwaraima kuwa, buqatata guda uku ce"

Bahlul: 1. Kakara mini shekaruna na duniya.

Sarki Harun: Wallahi bazan iyaba.

Bahlul: 2. Ka kareni daga mamayar mala'ikan mutuwa.

Sarki Harun: Wallahi bazan iyaba.

Bahlul: 3. ka sakani a aljannah ka nisanta ni daga wuta.

Haruna: Wallahi bazan iyaba.

Sai Bahlul yace masa:

"To wallahi kasani kai kanka abin mulkane, kai bamai mulki bane, don haka kasani bani da wata bukata a wajenka.

Tofa kunji mahaukaci mai hikima.

Wanne da darasi kuka dauka acikin wannan Qissa gameda shugabanninmu na yanzu ???