Tuesday, 19 December 2017

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA, YA MATSAYIN AURENSU ???

Tags

YA FURTA SAKI, AMMA MATARSA BA TA JI BA, YA MATSAYIN AURENSU ???

Tambayoyin TAFARKIN TSIRA:

Ass. Malam mutum ne ya furta saki ga matarsa amma bata jiba, shin ta saku ???

AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

To dan uwa matar tasaku, saboda sanin tasan an saketa bashi daga cikin sharudan saki.

Mutukar miji ya furta saki, mace tasaku koda bata jiba, yana daga cikin ka'idoji awajen malaman fiqhun musulunci:

Duk wanda ba'a damu da yardarsa ba wajan tabbatuwar abu, ba'a damuwa da saninsa.

Saboda haka yardar mace ba sharadi bace wajen zartuwar saki, haka ma saninta.

Dafatan Ma'aurata za'a dinga kiyayewa ana kai zuciya nesa.

Allah yayi mana mai kyau.