Wednesday, 20 December 2017

WANI MASOYIN ANNABI

Tags

Wani Mutum Yayi Tafiya Tare Da 'Dansa, Sai Rashin Lafiya Yakama Mahaifin Akan Hanyarsu, Kuma Cikin Dan Qankanin Lokaci Sai Ya Rasu.

Abin Mamaki Sai Yaron Yaga Kan Mahaifin nasa Ya Koma Na Alade.

Sai Hankalin Yaron Ya Tashi Yafara Kuka sosai Bisa Ga Wannan Musiba Da Ta Afkawa Mahaifin Sa.

Daga Karshe Sai Ya Maida Al'amarin Gaba Daya Zuwaga ALLAH, Yana Mai Kaskantar Da Kai Zuwa Gare Shi.

Yana ta Zaune Da Gawa Har Saida Barci Ya Kwashe Shi, Sai Yayi Mafarki Wani Mai Magana Yana Cewa dashi:-

"MAHAIFINKA YA KASANCE YANA CIN RIBA, AMMA ZAI SAMI CETON ANNABI (Sallallahu Alaihi wasallama).

SABODA BAI TABA JIN AN KIRAYI SUNAN SABA, SAI YAYI SALATI A GARE SHI.

DON HAKA AN MAYAR DASHI IZUWA SURAR SA TA FARKO".

(Mai neman Qarin bayani yaduba: Kitaab Mufidul Ulumi Wa Mubidul Humumi).

Fiye Da Hakan Ma ALLAH Zai Iya Yiwa Masu Salati Ga Masoyin Sa Sayyiduna RASULULLAH (Sallallahu alaihi Wasallama).

Ya ALLAH Ka Qara Narkar Da Mu, Kuma Ka Qarar Da Mu a Cikin sonsa.

Bari Muga Masu Rowa.

Muhammadur Rasulullah.