Wednesday, 20 December 2017

WANI HADISI MAI TSORATARWA GA DUK MUSULMI MAI IMANI:

Tags

WANI HADISI MAI TSORATARWA GA DUK MUSULMI MAI IMANI:

Wata rana manzon Allah (S.A.W) yazo kwanciya da daddare, sai Ummul- muminina, A'isha (R.A) ta tambaye shi, tace:

"Ya Rasulullah yanzu duk irin soyayya da kaunar da mata take yiwa mijinta, zaisa miji yatuna da ita a yinin Al-kiyama ?"

Sai manzon Allah (S.A.W) yace:

"In banda waje uku"

Sune kamar haka:

1. Wurin awun ayukka.

2. Wurin bayar da takardar sakamako.

3. Wurin hawan siradi.

Wannan hadisin yana karantar damu cewa a wuraren nan uku (3) wallahi Uwa bata tuna dan'ta, haka Da baya tuna iyayensa, mata bata tunawa da mijinta, haka miji baya tunawa da matarsa.

YA ALLAH KA SANYAMU CIKIN
RAHAMARKA A WURAREN NAN GUDA UKU (3).

DAN DARAJAR SAYYIDUNA MUHAMMAD RASULULLAH.