Tuesday, 19 December 2017

TUNATARWA GUDA 5 GA DUK MUSULMI MAIJIN TSORON ALLAH.

Tags

TUNATARWA GUDA 5 GA DUK MUSULMI MAIJIN TSORON ALLAH.

(1) Kazo Duniya Kana Kuka, Karshenka Za Ayi maka Kuka.

(2) Kazo Duniya Tsirara Sai a kayi maka Tufafi, Karshen ka Zaka koma Tsirara A kuma Yi maka Tufafi.

(3) A lokacin Da kazo Duniya Anyi maka Wanka, A lokacin da Zaka koma Za A kara Yi maka Wanka.

(4) A lokacin Da kazo Duniya Baka Iya tafiya ba, Sai dai A dauke ka, hakama lokacin da Zaka koma Saidai A dauke ka.

(5) Ranar da Kazo Duniya An Yi maka Kiran Sallah Batare da Anyi Sallah ba, A ranar Komawar ka ga UBANGIJI Za a yi maka Sallah Batare da An kira Sallah Ba.

Muna roqon Allah (S.W.T) yasa mucika da imani.