Tuesday, 19 December 2017

Kakula da wadannan abubuwa

Tags

Kada kayi gaba da mai son yin gaba dakai, idan ka ganshi kayi masa sallama.

Kada kadamu da hassadan mai hassada, bashshi muguntansa zata koma kansa.
****************

"Duk wanda yace duniya itace mafi mahimmanci a gareshi, To tabbas bakin cikinsa zai yawaita".
****************

kayi hakuri wurin barin sabon Allah, domin wani abun kanaso amma babu yadda zakayi, hakanan zaka bashshi don jin tsoron azabar Allah.
****************

"Ba abin alfahari bane don kayi rinjaye ga mai karfi, Abin alfahari shine ka yi adalci ga mai rauni".
****************

Wanda yafada maka magana mai zafi, kalma mai daci da 'kuna, mayar masa da tattausa mai taushi kamar ruwan sanyi.
****************

"ALLAH yabamu ikon ruqo da gaskiya!!