SU WANEN MUHAJIRUN ???
Siffar “Muhajir” tasamo asali ne daga kalmar “HIJRAH” wadda a harshen hausa take nufin QAURA.
Su kuwa Muhajirun anbasu wannan siffane saboda sun kauracewa gidajensu, da masaukansu; suka kyamaci zama tareda kafurai, ko kuma zamowa karkashin mulkinsu, saboda basu aminta daga fitinarsu ba.
Suka kaurace musu zuwa inda suka samu aminci da nutsuwa.
Kamar yadda Muminan farko (Sahabbai) suka kauracewa garin Makka zuwa birnin Madina.
[Kuduba Tafsirud’ Dabri: mujallady na 4 /318].
A yaren shari’a idan akace:
Muhajirun, to kai tsaye ana nufin Sahabban Ma’aiki (S.A.W) wadanda suka yi kaura daga Makkah zuwa Madina don su gudu da addininsu daga fadawa cikin fitinar kafurai da kafurci.
Hijira Sunna ce ta Annabawan da mutanensu suka saba musu a addini, Annabi Ibrahim ya kauracewa mutanensa, yace:
Ni mai yin hijira ne zuwa ga Ubangijina)
[Suratul Ankabut: 26].
Annabi Lud shima yayi hijira.
Annabi Musa ma yafita daga kasar Misra tareda mutanensa don tserewa fitina da kiriniya ta Fir’auna.
Annabi Muhammad (S.A.W) tareda Sahabbansa suma sunyi hijira zuwa garin Madina, kafin nan kuma yayiwa Sahabbansa izinin yin hijira zuwa kasar Habasha.
[Kuduba At Tahreer wat Tanweer: 10/84].
Hijirar da Ma’aiki (S.A.W) yayi ta zuwa Madina tareda Sahabbansa sifface babba data cancanci tarin yabo; don haka ne ma Ma’aiki SAW yake bayyanata a matsayin falala mai matukar girma, inda yake rarranshin Ansarawa yake cewa a hadisin da Abdullahi bn Zaid bn Asim (R.A) ya karbo yake cewa:
(Ba don dinbin falalar da take cikin hijira ba, da nima na zamo daya daga cikin Ansarawa (mutanen Madina).
[Kuduba Sahih Al Bukhari: 4330].
Sahabi baya cikin wannan siffa ta “Muhajir” harsai idan hijirar tasa da yayi ta zuwa Madina (Birnin Manzon Allah SAW) ta auku kafin bude garin Makka a shekara ta takwas (8) da hijirar Manzon Allah (SAW).
Dalilin hakan kuwa shine Hadisin da Ibnu Abbas (R.A) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW) yace:
(Babu sauran hijira [zuwa Madina da za’a baiwa mutum ladansa] bayan an riga an bude garin Makkah, abin da dai ya yi saura shine: Jihadi, da kuma ladan niyya).
[Kuduba Sahih Al Bukhari: 2783, ko sahih Muslim: 1353].
Wannan shine bayani takaitacce gameda “MUHAJIRUN”.
Allah kasa muyi koyi dasu muci albarkacinsu.