"KA SHAGALTU DA LAIFUKANKA KADA KA SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE"
Duk yayin da ka shagaltu da ganin laifukan mutane, kakutsa cikin neman inane kura-kuran mutane suke ???
Ma'ana: Kai baka yiwa kanka muhasaba (Hisabi), to, laifunka zasu yawaita batare daka ankara ba.
Masu iya magana suna cewa:
LAIFI TUDU NE.... Saika take naka sannan zaka hango na wani!
Duk mutumin da bai d'auki kansa mai laifi ba, baya dinga bibiyar irin aikin da yake aikatawa yana tantancewa, baya zama mai ganin kura-kuran kansa! To, lallai akwai nadama a qarshen rayuwarsa.
Domin kuwa zai tattara zunubai masu tarin yawa a kansa, tunda ya kawar da kansa daga ganin laifukansa, ya shagaltu da laifukan al'umma, ta inda ganinsa ya taqaitu ga ganin laifukan mutane.
'Yan'uwa mu gyara ayyukanmu, mu wanke zuqatanmu, mu rinqa yiwa kawunanmu hisabi, mu kasance masu tsanin tuhumar kawunanmu, tareda tuba daga munanan ayyukanmu, ta wannan sai mu kasance bayi na qwarai, dalilin haka sai Allah ya tausaya mana ya gafarta mana ya shigar damu cikin rahmarsa.
*********************
Ya Allah ka gafarta mana ka rabamu da son zuciya, ka shiryar damu hanya madaidaiciya, ka tabbatar damu a kan tafarkin tsira yazuwa Al-jannah.