HIKAYAR WASU MAKAFI GUDA UKU
Wasu maka'fi guda sun kasance suna zama suyi bara akan wata hanya da wata mata mai suna ummu jafar ke wucewa.
1. Daya daga cikinsu yana cewa:
Ya Allah ka azurtani dan darajarka.
2. Shikuma na biyun yakasance yana cewa:
Ya Allah ka azurtani don darajar ummu jafar.
kullum ummu jafar tanajin abinda suke fad'a.
Wata rana sai ummu jafar tariqa turowa wanda yake cewa ya Allah ka azurtani don falalarka da dirhami 2.
shikuma wanda yake cewa ya Allah ka azurtani don falalar ummu jafar saita turo masa da kaza soyayyiya kuma sai tasa dinare goma acikin cikin kazar.
kulum idan ta turo musu da wannan kyauta sai mai kaza yasiyarma abokin bararsa da kazar akan dirhami 2 wanda ummu jafar tabashi.
Haka sukai tayi har saida aka d'auki kwana 10
sannan ummu jafar tazo ta tambayi mai roqon Allah ya azurtashi da falalar ummu jafar cewa:
Bana azurtakaba, me kuma kake nema yanzu ???
Sai yace:
A'a nidai nasan kina aikomin da kaza har tsawon kwana 10 kuma idan kin turomin banaci, wannan maqocin nawa nake siyarma a dirhami 2 da kike bashi.
Sai tace masa ai acikin kowace kaza akwai dina're goma.
Sai ummu jafar tace:
Kaga wancan yanemi Allah ya azirtashi don falalata kuma na bashi amma sai aka hanashi wancan kuma yanemi Allah ya azirtashi da falalarsa kuma sai akabashi.
Saboda haka duk wanda ya dogara ga Allah (s.w.t) to babushi babu ta'bewa kuma bazai 'bata ba.
Ya Allah ka azurtamu da falalarka.
Tuesday, 19 December 2017
HIKAYAR WASU MAKAFI GUDA UKU
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)