Tuesday, 19 December 2017

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

Tags

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

Tambaya:

Assalam Malam inada Tambaya ?.

Shin idan an fara sallah kazo zakabi jam'i, zaka karanta addu'ar da ake yine bayan kabbarar harama ???

Amsa:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

To dan uwa abin da malamai suka fada shine:

Mutukar ya riski liman a mike, to zaiyi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, koda kuwa a raka'a ta biyu ne.

Saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare dashi, kuma addu'ar bude sallah zata fadi daga kansa, saboda wurin yinta yawuce.

Raka'ar da kafara samu tareda liman, ita ceraka'ar farko a wajenka, wannan yasa zakayi addu'ar bude sallah, koda kuwa shi liman a raka'a ta uku yake kota hudu.

Wannan shine zance mafi inganci.

Idan ka riski liman a tsaye amma abin daya rage yayi ruku'u, bazai isa ka karanta addu'ar bude sallah ba, sannan ka karanta Fatiha, to zaka karanta fatiha, kabar karanta addu'ar bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunnah ce, karanta fatiha ga mamu kuwa wajibice a wajan wasu malaman.

Domin neman Karin bayani sai kuduba Al-majmu'u na Nawawy mujallady na 3/276 da kuma Majmu'ul fataawa 30/150.

Allah shine mafi sani.