Tuesday, 19 December 2017

MENENE HUKUNCIN WANDA AKA YIWA KYAUTA BAI AMSA BA HARYA MUTU ???

Tags

MENENE HUKUNCIN WANDA AKA YIWA KYAUTA BAI AMSA BA HARYA MUTU ???

SHIN ZAI SHIGA RABON MAGADA ?

Assalamu alaikum.

Dan Allah malam Gawata tambayar gaggawa.

Wata baiwar Allah tasayi kaya da niyyar baiwa 'yar uwarta, amma kafin tabata sai 'yar uwar tarasu.

Shin wannan sayayya ta shiga cikin kayan gado ???

Nagode.

(Daga Asma'u Daheer)

Amsa:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

To 'yar uwa bazai shiga rabon magada ba, saboda kyauta bata tabbata sai an amsa.

Wannan yasa lokacin da sayyadina Abubakar yayiwa 'yarsa Aisha kyauta bata amsa ba, Har mutuwa tazo masa yasoke kyautar, ya mayar da ita dukiyar magada.

Kamar yadda Malik ya rawaito a MUWADDA'I a hadisi mai lamba ta :717.

Wannan itace maganar mafi yawancin malamai.

Domin neman Karin bayani kuduba : Al'umm na Shafi'I 4\64,da BADA'I USSANA'I'I. 6\8.

Wallahu A'alam.