Wednesday, 20 December 2017

FITINAR QABARI

Tags

Wata rana sayyidina uthman (R.A) yaje makabarta yana tsaye a bakin kabari yanata Zubarda hawaye yana kuka sai akace dashi ya uthman mezai tayar da hankalinka don kaga kabari, bayan ALLAH yagafarta maka da dukkan laifukan ka kuma yayi maka bishara da Aljannah tun kana raye a duniya ???.

Sai yace WALLAHI badan komai nake kukaba saidan naji da kunne na ANNABI (S.A.W) yana cewa:

Lallai kabari shine mazaunin farko na lahira, idan bawa ya tsira daga fitinar kabari abinda yake bayansa da sauki.

Wanda bai tsiraba abinda yake bayansa yafishi tsanani.

Muna fatan ALLAH ya tseratar damu daga fitinar Qabari.