Thursday, 15 June 2017

WANENE ABDULLAHI BN MAS'UD [RA] ???

Tags

WANENE ABDULLAHI BN MAS'UD [RA] ???
=====================

Abdullahi Bn Mas'ud Yana daya daga cikin wadanda suka fara musulunta tun kafin Annabi [S.A.W] yashiga gidan Arkam bn Abul Arkam.

Sababin musuluntar tasa kuwa shine a lokacin dayake kiwon dabbobi a Makka Annabi [SAW] yazo wucewa shida Abubakar [RA], sai ya tambaye shi yabasu nono.

Sai yace:

"Dukkan dabbobin basuda nono".

Sai Annabi [SAW] yasanya hannunsa ya ambaci sunan Allah take nonon ya bulbulo, dukkan su suka sha suka Qoshi.

Wannan abu da Abdullahi yagani sai mamaki ya
rufeshi, yace da Annabi [SAW].

"koya min abinda kafada haka ta kasance".

Sai Annabi [SAW] ya koyar dashi surori 70 daga bakinsa.

Yayi hijira sau 2, ya halarci yakin Badar da dukkan yaqoqi tareda Annabi [SAW].

Yana cikin manyan hadiman Annabi [SAW].

Shine gaba da kowa wajen iya karanta Al-qur'ani.

Shine Mutum na farko daya fara bayyanar da karatun alqur'ani a fili agaban mushrikan Makkah.

A zamanin Umar [RA] ya turashi kufa domin yadinga karantar dasu alqur'ani da hukuncin shari'ah.

Zan dakata anan.

Allah yakara masa yarda, sannan yaqara mana sonsu.

This Is The Oldest Page